Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 23 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 When you sit down to dine with a ruler, consider carefully what is before you, Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka,
2 and put a knife to your throat if you are a person ruled by appetite. ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne.
3 Do not crave his delicacies, for they are deceptive food. Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne.
4 Do not wear yourself out to get rich; have the wisdom to restrain yourself. Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.
5 The moment you look at wealth, it is gone, for it suddenly sprouts wings and flies off toward the heavens like an eagle. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.
6 Do not eat the bread of a stingy man, and do not crave his delicacies, Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;
7 for he is the kind of man who keeps counting the cost. "Eat and drink!" he says to you, but his heart is not with you. gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.
8 You will vomit up the little you have eaten and will have wasted your pleasant words. Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.
9 Do not speak in the hearing of a fool, for he will despise the wisdom of your words. Kada ka yi magana da wawa, gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a.
10 Do not move an ancient boundary stone or encroach on the fields of the fatherless, Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu,
11 for their Redeemer is strong; our Father will take up their cause against you. gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu.
12 Apply your heart to instruction and your ears to words of knowledge. Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.
13 Do not withhold discipline from a child; if you strike him with the rod, he will not die. Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.
14 Strike him with the rod, and you will deliver his soul from the grave. Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.
15 My son, if your heart is wise, my own heart will be glad as well. Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna;
16 My inmost being will rejoice when your lips speak what is right. cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.
17 Do not let your heart envy sinners, but continue in the fear of our Father all day long. Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.
18 Surely there is a future, and your hope will not be cut off. Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
19 Hear, my son, and be wise, and keep your heart on the right road. Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.
20 Do not be among those who get drunk on wine or those who gorge themselves on meat, Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,
21 for the drunkard and the glutton will come to poverty, and drowsiness will clothe them in rags. gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.
22 Listen to your father, who gave you life, and do not despise your mother when she is old. Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
23 Buy truth and do not sell it; buy wisdom, instruction, and understanding. Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi.
24 The father of a righteous child will greatly rejoice; whoever fathers a wise son will delight in him. Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.
25 Let your father and mother be glad; let her who gave you birth rejoice. Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!
26 My son, give me your heart, and let your eyes delight in my ways. Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,
27 For a prostitute is a deep pit, and an adulterous woman is a narrow well. gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.
28 She lies in wait like a robber and leads many men into faithlessness. Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.
29 Who has misery? Who has sorrow? Who has strife? Who has complaints? Who has wounds for no reason? Who has bleary eyes? Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?
30 Those who linger long over wine, those who go to sample bowls of mixed wine. Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.
31 Do not gaze at wine while it is red, while it sparkles in the cup and goes down smoothly. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!
32 In the end it bites like a serpent and stings like a viper. A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.
33 Your eyes will see strange things, and your heart will utter twisted things. Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.
34 You will be like one lying down in the heart of the sea, like one lying on the top of a ship's mast. Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa.
35 "They struck me, but I felt no pain; they beat me, but I did not know it. When will I wake up? I will look for another drink." Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]