Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 24 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Do not envy evil men, and do not desire to be with them, Kada ka yi ƙyashin mugaye, kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu;
2 for their hearts plot violence, and their lips speak of trouble. gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne.
3 By wisdom a house is built, and by understanding it is established; Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
4 and by knowledge its rooms are filled with all precious and pleasant riches. ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja.
5 A wise man is full of strength, and a man of knowledge increases his power, Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;
6 for by wise guidance you can wage your war, and victory comes through many counselors. don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.
7 Wisdom is too high for a fool; at the gate, he has nothing to say. Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.
8 Whoever plans to do evil will be called a schemer. Duk mai ƙulla mugunta za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne.
9 A fool's scheming is sin, and the scoffer is detestable to people. Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.
10 If you falter in a time of trouble, your strength is small. In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai!
11 Rescue those being taken away to death, and hold back those stumbling toward the slaughter. Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka.
12 If you say, "Look, we did not know this," does not he who weighs the heart perceive it? Does not he who watches over your soul know it? And will he not repay each person according to his deeds? In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?
13 My son, eat honey, for it is good, and the honeycomb's drippings are sweet to your taste. Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau; zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.
14 Know that wisdom is just like this to your soul; if you find it, there is a future, and your hope will not be cut off. Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai; in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
15 Do not lie in wait, you wicked man, against the home of the righteous; do not destroy his resting place, Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali, kada ka ƙwace masa wurin zama;
16 for though the righteous falls seven times, he rises again, but the wicked stumble in disaster. gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma, amma bala’i kan kwantar da mugaye.
17 Do not rejoice when your enemy falls, and do not let your heart be glad when he stumbles, Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi; sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki,
18 lest our Father see it and be displeased, and turn his anger away from him. in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi.
19 Do not fret because of evildoers, and do not envy the wicked, Kada ka ji tsoro saboda masu mugunta ko ka yi ƙyashin mugaye,
20 for the evil man has no future; the lamp of the wicked will be snuffed out. gama mugu ba shi da zuciya ta nan gaba, kuma fitilar mugaye za tă mutu.
21 My son, fear our Father and the king, and do not join with those who rebel against them, Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa,
22 for their disaster will rise suddenly, and who knows the ruin that both of them can bring? gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa?
23 These also are sayings of the wise: Showing partiality in judgment is not good. Waɗannan ma maganganun masu hikima ne, Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau.
24 Whoever says to the guilty, "You are innocent," peoples will curse him and nations will denounce him, Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”, mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba.
25 but it will go well for those who convict the guilty, and a rich blessing will come upon them. Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi, kuma babban albarka zai zo a kansu.
26 An honest answer is like a kiss on the lips. Amsa da take ta gaskiya tana kamar sumba a leɓuna.
27 Prepare your work outside, get your fields ready, and after that build your house. Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka.
28 Do not be a witness against your neighbor without cause; would you deceive with your lips? Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.
29 Do not say, "I will do to him as he did to me; I will pay the man back for what he has done." Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini; zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.”
30 I passed by the field of a lazy man, by the vineyard of someone lacking sense, Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;
31 and there it was, all overgrown with thorns; the ground was covered with weeds, and its stone wall was broken down. ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.
32 Then I looked and took it to heart; I saw and received instruction. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.
33 A little sleep, a little slumber, a little folding of the hands to rest, Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
34 and poverty will come upon you like a robber, and scarcity like an armed man. sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]