Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 25 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 These also are proverbs of Solomon, which the men of Hezekiah king of Judah copied out. Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara.
2 It is the glory of our Father to conceal a matter, but the glory of kings to search a matter out. Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne.
3 As the heavens are high and the earth is deep, so the heart of kings is unsearchable. Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika.
4 Take away the dross from the silver, and a vessel comes forth for the refiner. Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa;
5 Take away the wicked from before the king, and his throne will be established in righteousness. ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci.
6 Do not put yourself forward in the king's presence, and do not stand in the place of the great; Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki, kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane;
7 for it is better to be told, "Come up here," than to be put in a lower place in front of a noble you can see. gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka
8 Do not rush into a quarrel, for what will you do in the end when your neighbor puts you to shame? kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya?
9 Argue your case with your neighbor himself, but do not disclose another's secret, In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani,
10 lest the one who hears it shame you, and your bad reputation never goes away. in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba.
11 A word spoken at the right moment is like apples of gold in settings of silver. Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa.
12 Like a ring of gold or an ornament of fine gold is wise correction to a listening ear. Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.
13 Like the cold of snow in the time of harvest is a faithful messenger to those who send him; he refreshes the soul of his masters. Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi.
14 Like clouds and wind without rain is one who boasts of a gift never given. Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa.
15 By patience a ruler is persuaded, and a soft tongue breaks bone. Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi.
16 If you find honey, eat only enough, or you will have too much and vomit. In ka sami zuma, ka sha isashe kawai, in ya yi yawa, za ka yi amai.
17 Don't visit your neighbor's house too often, or he will grow weary of you and hate you. Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka.
18 Like a club, a sword, and a sharp arrow is one who bears false witness against his neighbor. Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.
19 Like a bad tooth or a foot out of joint is trust in a faithless person in time of trouble. Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala.
20 Like one who takes off a garment on a cold day, like vinegar poured on baking soda, is the one who sings songs to a heavy heart. Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki.
21 If your enemy is hungry, give him bread to eat, and if he is thirsty, give him water to drink; In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha.
22 for you will heap coals of fire on his head, and our Father will reward you. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka.
23 The north wind brings forth rain, and a secretive tongue, angry looks. Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.
24 It is better to live in a corner of the rooftop than in a shared house with a quarrelsome wife. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
25 Like cold water to a weary soul is good news from a distant land. Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa.
26 Like a muddied spring or a polluted fountain is a righteous person who gives way before the wicked. Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye.
27 It is not good to eat too much honey, nor to seek your own glory. Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa, haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka.
28 Like a city broken into and left without walls is a person who has no control over his own spirit. Kamar birni da katangarsa sun rushe haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]