Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 26 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Like snow in summer and like rain at harvest, honor is not fitting for a fool. Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba.
2 Like a fluttering sparrow or a darting swallow, an undeserved curse does not come to rest. Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.
3 A whip for the horse, a bridle for the donkey, and a rod for the backs of fools. Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye!
4 Do not answer a fool according to his foolishness, or you yourself will be like him. Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.
5 Answer a fool according to his foolishness, or he will be wise in his own eyes. Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.
6 Whoever sends a message through a fool cuts off his own feet and drinks down violence. Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.
7 Like the legs of a lame man hanging useless is a proverb in the mouth of fools. Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas haka karin magana yake a bakin wawa.
8 Like binding a stone in a sling is giving honor to a fool. Kamar ɗaura dutse a majajjawa haka yake da girmama wawa.
9 Like a thornbush in the hand of a drunkard is a proverb in the mouth of fools. Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa.
10 Like an archer who wounds everyone is one who hires a fool or hires any passerby. Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.
11 As a dog returns to its vomit, so a fool repeats his foolishness. Kamar yadda kare kan koma ga amansa, haka wawa kan maimaita wautarsa.
12 Do you see someone wise in his own eyes? There is more hope for a fool than for him. Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.
13 The lazy person says, "There is a lion in the road! A lion in the streets!" Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
14 As a door turns on its hinges, so the lazy person turns on his bed. Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa.
15 The lazy person buries his hand in the dish; it wearies him to bring it back to his mouth. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.
16 The lazy person is wiser in his own eyes than seven who answer wisely. Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.
17 Like grabbing a dog by the ears is a passerby who meddles in a quarrel not his own. Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.
18 Like a madman shooting firebrands, arrows, and death, Kamar yadda mahaukaci yake harbin cukwimai ko kibiyoyi masu dafi
19 so is the one who deceives his neighbor and says, "I was only joking!" haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”
20 Without wood a fire goes out, and without a gossip a quarrel dies down. In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.
21 As charcoal to embers and wood to fire, so a quarrelsome person kindles strife. Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.
22 The words of a gossip are like choice morsels; they sink down into the inmost parts. Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum.
23 Like a glaze covering an earthen pot are smooth lips with an evil heart. Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba haka leɓuna masu mugun zuciya.
24 An enemy disguises himself with his lips, but in his heart he harbors deceit. Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa, amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci
25 When he speaks graciously, do not believe him, for seven abominations fill his heart. Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi, gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.
26 Though his hatred is hidden by deceit, his wickedness will be exposed in the assembly. Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya, duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.
27 Whoever digs a pit will fall into it, and a stone rolls back on the one who rolls it. In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki; in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.
28 A lying tongue hates those it crushes, and a flattering mouth works ruin. Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]