Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 27 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Do not boast about tomorrow, for you do not know what a day may bring. Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.
2 Let someone else praise you, and not your own mouth; a stranger, and not your own lips. Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba.
3 A stone is heavy and the sand a burden, but a fool's provocation is heavier than both. Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.
4 Wrath is cruel and anger is overwhelming, but who can stand before jealousy? Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?
5 Open rebuke is better than love that stays hidden. Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye.
6 A friend's wounds are faithful, but an enemy's kisses are deceitful. Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
7 A well-fed person tramples honeycomb, but to the hungry even what is bitter tastes sweet. Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.
8 A man who strays from his home is like a bird that strays from its nest. Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa haka yake da mutumin da ya bar gidansa.
9 Oil and incense gladden the heart, and the sweetness of a friend comes from heartfelt counsel. Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
10 Do not forsake your friend or your father's friend, and do not go to your brother's house when disaster strikes; better a neighbor nearby than a brother far off. Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
11 Be wise, my son, and make my heart glad, so that I can answer anyone who taunts me. Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.
12 The prudent sees danger and takes cover, but the simple keep going and pay the price. Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce, marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
13 Take the garment of one who puts up security for a stranger; hold it as collateral when he does so for a foreign woman. A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
14 Whoever blesses his neighbor with a loud voice early in the morning, it will be taken as a curse. In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana.
15 A quarrelsome wife is like a constant dripping on a rainy day. Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;
16 Restraining her is like restraining the wind, or grasping oil with the right hand. hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka.
17 Iron sharpens iron, and one person sharpens another. Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.
18 Whoever tends a fig tree will eat its fruit, and whoever guards his master will be honored. Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.
19 As water reflects the face, so the heart reflects the person. Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.
20 The grave and Destruction are never satisfied, and a person's eyes are never satisfied. Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani.
21 The crucible is for silver and the furnace for gold, and a person is tested by the praise he receives. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.
22 Though you grind a fool in a mortar with a pestle, along with the grain, his foolishness will not leave him. Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.
23 Know well the condition of your flocks, and give careful attention to your herds. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;
24 For riches do not last forever, nor does a crown endure to every generation. domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.
25 When the grass is gone and the new growth appears and the mountain herbs are gathered, Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,
26 the lambs will provide your clothing, and the goats will provide the price of a field; gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.
27 and there will be enough goats' milk for your food, for the food of your household and to sustain your servant girls. Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]