Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 28 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The wicked flee when no one pursues, but the righteous are as bold as a lion. Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki.
2 When a land rebels, it has many rulers, but with a man of understanding and knowledge, it stays stable. Sa’ad da ƙasa ta yi tayarwa, takan kasance da masu mulki da yawa, amma mai fahimi da sani kan mai da zaman lafiya.
3 A poor man who oppresses the helpless is like a driving rain that leaves no food. Mai mulkin da ya danne talakawa yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi.
4 Those who forsake the law praise the wicked, but those who keep the law strive against them. Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.
5 Evil people do not understand justice, but those who seek our Father understand it fully. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.
6 Better is a poor man who walks with integrity than a rich man crooked in his ways. Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne.
7 Whoever keeps the law is a son with understanding, but a companion of gluttons shames his father. Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari, amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya.
8 Whoever multiplies his wealth by interest and unjust gain gathers it for one who is generous to the poor. Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.
9 If anyone refuses to listen to the law, even his prayer is detestable. In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.
10 Whoever leads the upright astray down an evil path will fall into his own pit, but the blameless will inherit good things. Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.
11 A rich man is wise in his own eyes, but a poor man with understanding sees right through him. Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai.
12 When the righteous triumph, there is great glory, but when the wicked rise, people go into hiding. Sa’ad da adalai suka yi nasara, kowa yakan yi biki; amma sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya.
13 Whoever conceals his sins will not prosper, but whoever confesses and turns from them will find mercy. Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.
14 Blessed is the one who always remains reverent, but whoever hardens his heart will fall into calamity. Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah, amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.
15 Like a roaring lion or a charging bear is a wicked ruler over a helpless people. Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake.
16 A ruler who lacks understanding is a cruel oppressor, but whoever hates unjust gain will prolong his days. Mugu mai mulki ba shi da azanci, amma duk wanda yake ƙin ƙazamar riba yakan yi tsawon rai.
17 A man weighed down by the guilt of bloodshed will be a fugitive until death; let no one support him. Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa; kada wani ya taimake shi.
18 Whoever walks in integrity will be kept safe, but whoever is crooked in his ways will suddenly fall. Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya, amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.
19 Whoever works his land will have plenty of bread, but whoever chases empty pursuits will have plenty of poverty. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.
20 A faithful man will abound with blessings, but whoever rushes to get rich will not go unpunished. Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci.
21 Showing partiality is not good, yet for a piece of bread a man will do wrong. Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa.
22 A stingy man rushes after wealth and does not know that poverty will overtake him. Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki bai san cewa talauci ne ke jiransa ba.
23 Whoever rebukes a man will in the end find more favor than one who flatters with his tongue. Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe fiye da wanda yake mai daɗin baki.
24 Whoever robs his father or mother and says, "It is no sin," is a companion to one who destroys. Duk wanda ya yi wa mahaifin ko mahaifiyarsa sata ya kuma ce, “Ai, ba laifi ba ne” abokin mai hallakarwa ne shi.
25 A greedy man stirs up strife, but whoever trusts in our Father will be enriched. Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara.
26 Whoever trusts in his own heart is a fool, but whoever walks in wisdom will be kept safe. Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.
27 Whoever gives to the poor will lack nothing, but whoever closes his eyes to them will receive many curses. Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.
28 When the wicked rise, people go into hiding, but when they perish, the righteous flourish. Sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya; amma sa’ad da mugu ya hallaka, adali kan ci gaba cikin arziki da lafiya.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]