Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 29 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Whoever is often corrected yet refuses to listen will suddenly be broken beyond healing. Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa.
2 When the righteous flourish, the people rejoice, but when the wicked rule, the people groan. Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi.
3 A man who loves wisdom brings joy to his father, but a companion of prostitutes squanders his wealth. Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.
4 By justice a king gives a land stability, but one who is greedy for bribes tears it down. Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.
5 A man who flatters his neighbor spreads a net for his feet. Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki yana sa wa ƙafafunsa tarko ne.
6 An evil man is snared by his own sin, but the righteous sing and rejoice. Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa, amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna.
7 The righteous care about justice for the poor, but the wicked have no such understanding. Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa, amma mugaye ba su da wannan damuwa.
8 Mockers set a city ablaze, but the wise calm the anger. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.
9 When a wise man goes to court with a fool, the fool rages and scoffs, and there is no peace. In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.
10 The bloodthirsty hate the blameless and seek to kill the upright. Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.
11 A fool vents all his anger, but a wise man holds it back and keeps himself calm. Wawa yakan nuna fushinsa a fili, amma mai hikima kan kanne fushinsa.
12 If a ruler listens to lies, all his officials become wicked. In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.
13 The poor man and the oppressor have this in common: our Father gives sight to the eyes of both. Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani.
14 If a king judges the poor with fairness, his throne will be established forever. In sarki yana hukunta talakawa da adalci kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.
15 The rod and a word of correction give wisdom, but a child left to himself brings shame to his mother. Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
16 When the wicked flourish, wrongdoing flourishes, but the righteous will see the wicked's downfall. Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa, amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.
17 Discipline your son, and he will give you peace; he will bring delight to your heart. Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama; zai ba ka farin cikin da kake so.
18 Where there is no revelation, the people run wild, but blessed is the one who keeps the law. Inda ba wahayi, mutane kan kangare; amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka.
19 A servant cannot be corrected by words alone; though he understands, he will not obey. Ba a yi wa bawa gyara ta wurin magana kawai; ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
20 Do you see a man who is hasty with his words? There is more hope for a fool than for him. Ka ga mutum mai yin magana da garaje? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
21 Pamper a servant from childhood, and in the end he will become like an heir. In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro, zai jawo baƙin ciki a ƙarshe.
22 An angry man stirs up strife, and a hot-tempered man commits many sins. Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa, mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa.
23 A man's pride brings him low, but a humble spirit gains honor. Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.
24 An accomplice of a thief is his own enemy; he hears the curse but says nothing. Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne; yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba.
25 Fear of man lays a snare, but whoever trusts in our Father is kept safe. Jin tsoron mutum tarko ne, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
26 Many seek a ruler's favor, but justice for a person comes from our Father. Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki, amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.
27 An unjust man is detestable to the righteous, and an upright person is detestable to the wicked. Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya; mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]