Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 30 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The words of Agur son of Jakeh—the oracle. The man declares: I am weary, O my Father; I am weary, O my Father, and worn out. Maganganun Agur ɗan Yake, magana ce horarriya. Wannan mutum ya furta wa Itiyel da kuma ga Ukal,
2 Surely I am too brutish to be a man; I do not have the understanding of a man. “Ni ne mafi jahilci a cikin mutane; ba ni da fahimi irin na mutum.
3 I have not learned wisdom, nor do I have knowledge of the Holy One. Ban koyi hikima ba, ba ni kuma da sani game da Mai Tsarkin nan,
4 Who has ascended to heaven and come down? Who has gathered the wind in the hollow of his hands? Who has wrapped the waters in a garment? Who has established all the ends of the earth? What is his name, and what is his son's name? Surely you know! Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani!
5 Every word of our Father proves true; he is a shield to those who take refuge in him. “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
6 Do not add to his words, or he will rebuke you and prove you a liar. Kada ka ƙara ga maganarsa, in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne.
7 Two things I ask of you; do not withhold them from me before I die: “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji; kada ka hana ni kafin in mutu.
8 Keep falsehood and lies far from me; give me neither poverty nor riches; feed me only the bread that is my portion, Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.
9 for if I am full, I may deny you and say, "Who is God?" or if I am poor, I may steal and profane the name of my God. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.
10 Do not slander a servant to his master, or he will curse you and you will be found guilty. “Kada ka baza ƙarairayi game da bawa ga maigidansa, in ba haka ba, zai la’ance ka, za ka kuwa sha wahala a kan haka.
11 There is a generation that curses its father and does not bless its mother. “Akwai waɗanda sukan zagi mahaifinsu ba sa kuma sa wa mahaifiyarsu albarka;
12 There is a generation clean in its own eyes yet not washed of its filth. waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su;
13 There is a generation—how proud its eyes, how scornful its glances! waɗanda kullum idanunsu masu kallon reni ne, waɗanda kallon da suke yi na daurin gira ne;
14 There is a generation whose teeth are swords, whose fangs are knives, to devour the poor from the earth and the needy from among mankind. waɗanda haƙoransu takuba ne waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne don su cinye matalauta daga duniya da kuma mabukata daga cikin mutane.
15 The leech has two daughters: "Give" and "Give." Three things are never satisfied; four never say, "Enough": “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’
16 The grave, the barren womb, the land never satisfied with water, and the fire that never says, "Enough." Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’
17 The eye that mocks a father and scorns to obey a mother—the ravens of the valley will pluck it out, and the young vultures will eat it. “Idon da yake yi wa mahaifi ba’a, wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya, hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido, ungulai za su cinye su.
18 Three things are too wonderful for me; four I do not understand: “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,
19 the way of an eagle in the sky, the way of a serpent on a rock, the way of a ship in the heart of the sea, and the way of a man with a young woman. yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.
20 This is the way of an adulteress: she eats and wipes her mouth and says, "I have done no wrong." “Ga yadda mazinaciya take yi. Takan ci ta share bakinta ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’
21 Under three things the earth trembles; under four it cannot bear up: “Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki, abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa,
22 a servant when he becomes king, and a fool when he is filled with food; bawan da ya zama sarki, wawan da ya ƙoshi da abinci,
23 an unloved woman when she finally marries, and a servant girl when she displaces her mistress. macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji, da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta.
24 Four things on earth are small, yet they are exceedingly wise: “Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana, duk da haka suna da hikima ƙwarai.
25 the ants are a people not strong, yet they store up their food in the summer; Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;
26 the rock badgers are a people not mighty, yet they make their homes in the cliffs; remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;
27 the locusts have no king, yet all of them advance in ranks; fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;
28 the lizard you can catch in your hands, yet it is found in kings' palaces. ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.
29 Three things are stately in their stride; four are stately in their walk: “Akwai abubuwa uku da suke jan jiki da kuma taƙama a tafiyarsu abubuwa huɗu waɗanda suke kwarjini da taƙama a tafiyarsu,
30 the lion, mightiest among beasts, which turns back before nothing; zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa;
31 the strutting rooster, the male goat, and a king whose army is with him. zakara mai taƙama, da bunsuru, da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi.
32 If you have been foolish, exalting yourself, or if you have schemed evil, put your hand over your mouth. “In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka, ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta, ka dāfa hannunka a bisa bakinka!
33 For pressing milk produces curds, pressing the nose produces blood, and pressing anger produces strife. Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]