Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 31 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The words of King Lemuel—an oracle his mother taught him: Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya mahaifiyarsa ta koya masa,
2 What, my son? What, son of my womb? What, son of my vows? “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!
3 Do not give your strength to women, or your ways to those who destroy kings. Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata, ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.
4 It is not for kings, Lemuel—not for kings to drink wine, or for rulers to crave strong drink. “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,
5 For if they drink, they will forget what is decreed and pervert the rights of all the oppressed. don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.
6 Give strong drink to one who is perishing, and wine to those in bitter distress. A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;
7 Let them drink and forget their poverty, and remember their misery no more. bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
8 Open your mouth for the voiceless, for the rights of all who are left destitute. “Yi magana domin bebaye, domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
9 Open your mouth, judge righteously, and defend the rights of the poor and needy. Yi magana a kuma yi shari’ar adalci; a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”
10 A woman of valor—who can find her? She is far more precious than jewels. Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
11 The heart of her husband trusts in her, and he will lack nothing of value. Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
12 She does him good and not harm, all the days of her life. Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta.
13 She seeks out wool and flax, and works with willing hands. Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.
14 She is like the merchant ships, bringing her food from afar. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.
15 She rises while it is still night, provides food for her household, and portions for her servant girls. Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
16 She considers a field and buys it; from the fruit of her hands she plants a vineyard. Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
17 She wraps herself in strength and makes her arms strong. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
18 She perceives that her trading is profitable; her lamp does not go out at night. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
19 She puts her hands to the spinning staff, and her hands grasp the spindle. Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.
20 She opens her hand to the poor and reaches out her hands to the needy. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.
21 She has no fear for her household when it snows, for all her household are clothed in scarlet. Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.
22 She makes coverings for herself; her clothing is fine linen and purple. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
23 Her husband is known in the gates, when he sits among the elders of the land. Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari.
24 She makes linen garments and sells them, and supplies sashes to the merchants. Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.
25 Strength and dignity are her clothing, and she laughs at the days to come. Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.
26 She opens her mouth with wisdom, and faithful instruction is on her tongue. Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.
27 She watches over the ways of her household and does not eat the bread of idleness. Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
28 Her children rise up and call her blessed; her husband also, and he praises her: ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,
29 "Many daughters have done valiantly, but you surpass them all." “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo, amma ke kin fi su duka.”
30 Charm is deceptive and beauty is fleeting, but a woman who reveres our Father—she will be praised. Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
31 Give her the fruit of her hands, and let her works praise her in the gates. Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]