Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Ecclesiastes 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The words of the Teacher, son of David, king in Jerusalem. Kalmomin Malami, ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima.
2 "Utterly fleeting," says the Teacher, "utterly fleeting! Everything is fleeting." “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami. “Gaba ɗaya ba amfani! Kome ba shi da amfani!”
3 What does a person gain from all the labor at which they toil under the sun? Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar da yake fama a duniya?
4 A generation goes, and a generation comes, but the earth remains forever. Zamanai sukan zo zamanai su wuce, amma duniya tana nan har abada.
5 The sun rises and the sun sets, and hurries back to the place where it rises. Rana takan fito rana ta kuma fāɗi, ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
6 The wind blows to the south and turns to the north; round and round it goes, ever returning on its circuits. Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
7 All the streams run to the sea, yet the sea is never full; the streams return to their source and flow again. Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika. Daga inda rafuffukan suke fitowa, a can suke komawa kuma.
8 All things are wearisome, more than anyone can express; the eye is not satisfied with seeing, nor the ear filled with hearing. Dukan abubuwa suna kawo gajiya, gaban magana. Ido ba ya gaji da gani, haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
9 What has been is what will be, and what has been done is what will be done; there is nothing new under the sun. Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance, abin da aka yi za a sāke yi kuma; babu wani abu sabo a duniya.
10 Is there anything anyone can point to and say, "Look, this is new"? It was already here, in the ages before us. Akwai wani abin da za a ce, “Duba! Ga wani abu sabo”? Abin yana nan, tun dā can, ya kasance kafin lokacinmu.
11 There is no remembrance of those who came before, and even those yet to come will not be remembered by those who follow them. Ba a tunawa da mutanen dā, haka su ma da ba a haifa ba tukuna waɗanda za su biyo bayansu ba za a tuna da su ba.
12 I, the Teacher, was king over Israel in Jerusalem. Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima.
13 I gave my heart to seek and explore by wisdom all that is done under heaven—a miserable task God has given mankind to struggle with. Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane!
14 I saw all the deeds done under the sun, and look—it is all fleeting, a chasing after wind. Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.
15 What is crooked cannot be made straight, and what is lacking cannot be counted. Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba; ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.
16 I told myself, "Look, I have grown great and gained more wisdom than all who ruled Jerusalem before me; my heart has seen much wisdom and knowledge." Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.”
17 I set my mind to know wisdom, and madness and foolishness; I learned this too is a chasing after the wind. Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.
18 For with much wisdom comes much grief, and the more knowledge, the more sorrow. Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki; yawan sani, yawan ɓacin rai.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]