Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Ecclesiastes 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In my heart I said, "Come, I'll test you with pleasure; enjoy what's good." But this too was fleeting. Na ce wa kaina, “Zo, zan gwada ka da jin daɗi don in ga abin da yake da kyau.” Amma wannan ma ya zama ba amfani.
2 I said of laughter, "It is madness," and of pleasure, "What does it accomplish?" Sai na ce, “Dariya hauka ce. Kuma me jin daɗi yake kawowa?”
3 I explored in my heart how to cheer my body with wine—my heart still guiding me with wisdom—and to grasp foolishness, until I might see what is good for people to do under heaven the few days of their lives. Na yi ƙoƙari in sa raina yă yi farin ciki da ruwan inabi, in kuma rungumi wauta, hankalina kuma yana yin mini jagora da hikima. Na so in ga abin da yake da daraja ga mutane a duniya a ’yan kwanakinsu.
4 I undertook great works. I built houses for myself and planted vineyards. Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi.
5 I made myself gardens and parks, and planted in them all kinds of fruit trees. Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu.
6 I made myself pools of water to irrigate a forest of growing trees. Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa.
7 I bought male and female slaves, and had home-born slaves too. I owned larger herds and flocks than anyone before me in Jerusalem. Na sayi bayi mata da maza, ina kuma da waɗansu bayin da aka haifa a gidana. Ina da garkunan shanu da na tumaki da na awaki fiye da duk wanda ya taɓa zama a Urushalima kafin ni.
8 I gathered for myself silver and gold, the treasure of kings and provinces. I got male and female singers, and men's delights—many concubines. Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so.
9 So I became great, greater than all before me in Jerusalem; and my wisdom stayed with me. Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba.
10 Whatever my eyes wanted I did not withhold. I refused my heart no joy, for my heart delighted in all my work, and this was my reward for all my work. Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba; ban hana zuciyata wani jin daɗi ba. Zuciyata ta yi murna da dukan aikina, wannan kuwa shi ne ladan dukan famata.
11 Then I surveyed all my hands had done and the toil I spent doing it, and it was all fleeting, chasing wind; nothing was gained under the sun. Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana, da abin da na yi fama don in samu, sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai; babu wata riba a duniya.
12 So I turned to consider wisdom, madness, and foolishness. For what can the king's successor do? Only what has already been done. Sai na juya ga tunanina don in lura da hikima, da kuma hauka da wauta. Me ya rage wa magājin sarki yă yi fiye da abin da aka riga aka yi?
13 I saw that wisdom has more gain than foolishness, as light has more than darkness. Na ga cewa hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.
14 The wise person has eyes in his head, but the fool walks in darkness. And yet I perceived that the same fate befalls them all. Mai hikima ya san inda ya nufa, wawa kuwa yana tafiya a cikin duhu; amma sai na gane cewa ƙaddara ɗaya ce take samunsu.
15 Then I thought, "The fool's fate is mine too. So why have I been so very wise?" And I decided this too is fleeting. Sai na yi tunani a zuciyata, “Ƙaddarar wawa za tă same ni ni ma. Wace riba ce hikimata za tă jawo mini?” Na ce a zuciyata, “Wannan ma ba shi da amfani.”
16 The wise, like the fool, will not be remembered for long; in days to come both are forgotten. How the wise die just like fools! Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba; nan gaba za a manta da su. Yadda wawa zai mutu, haka ma mai hikima!
17 So I hated life, because the work done under the sun grieved me; it is all fleeting, a chasing after wind. Don haka na ƙi jinin rayuwa, gama aikin da ake yi a duniya yana ɓata mini rai. Dukan abin da yake cikinta kuwa ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
18 I hated all my labor under the sun, since I must leave it to the one after me. Na ƙi jinin dukan abubuwan da na yi wahala ina yi a duniya, gama dole in bar su wa na bayana.
19 Who knows if he will be wise or a fool? Yet he will control all I worked for with my wisdom under the sun. This too is fleeting. Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani.
20 So I gave my heart up to despair over all the toil I labored at under the sun. Saboda haka zuciyata ta fara karaya a kan dukan faman aikina a duniya.
21 One may work with wisdom, knowledge, and skill, yet must leave it all to be enjoyed by someone who never worked for it. This too is fleeting, a great evil. Gama mutum zai yi aikinsa da dukan hikimarsa, da saninsa, da gwanintarsa, sa’an nan dole yă bar dukan abin da ya mallaka ga wani wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma ba shi da amfani, hasara ce mai yawa.
22 What does a person gain from all the toil and striving of heart he labors at under the sun? Me mutum zai samu daga aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin a duniya?
23 All his days bring sorrow, his work grief; even at night his mind gets no rest. This too is fleeting. Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani.
24 Nothing is better for a person than to eat, drink, and enjoy his work. This too, I saw, is from God's hand, Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne,
25 for apart from him, who can eat or who can find enjoyment? gama in ba tare da shi ba, wa zai iya ci yă sha yă kuma ji daɗi?
26 God gives wisdom, knowledge, and joy to the person who pleases him, but to the sinner he gives the work of gathering and collecting, only to hand it to one who pleases God. This too is fleeting, chasing wind. Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]