Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Ecclesiastes 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 For everything there is a season, and a time for every matter under heaven: Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2 a time to be born, and a time to die; a time to plant, and a time to uproot what is planted; Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3 a time to kill, and a time to heal; a time to tear down, and a time to build up; Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4 a time to weep, and a time to laugh; a time to mourn, and a time to dance; Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.
5 a time to throw away stones, and a time to gather stones together; a time to embrace, and a time to refrain from embracing; Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su, lokacin runguma da lokacin dainawa.
6 a time to seek, and a time to lose; a time to keep, and a time to throw away; Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya, lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7 a time to tear, and a time to sew; a time to be silent, and a time to speak; Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.
8 a time to love, and a time to hate; a time for war, and a time for peace. Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.
9 What gain has the worker from his toil? Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa?
10 I have seen the task that God has given people to keep them busy. Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane.
11 He made everything beautiful in its time, and set eternity in the human heart—yet no one can grasp what God has done from start to end. Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.
12 I know nothing is better for them than to enjoy life and do good while they live. Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai.
13 Also, that everyone eat, drink, and find satisfaction in all their work—this is God's gift. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.
14 I know all God does lasts forever; nothing can be added, nothing removed. He has done it so people will fear before him. Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.
15 What is has already been, and what will be has already been; and God seeks out what was driven away. Duk abin da yana nan ya taɓa kasancewa, kuma abin da zai kasance, ya taɓa kasancewa; Allah kuma zai nemi bayanin abubuwan da suka wuce.
16 I also saw under the sun: evil in the place of judgment, and evil in the place of righteousness. Sai na ga wani abu kuma a duniya, a wurin shari’a, akwai mugunta a can, a wurin adalci, akwai mugunta a can.
17 I said in my heart: "God will judge the righteous and the wicked, for there's a time for every matter and every deed, there." Sai na yi tunani a zuciyata, “Allah zai shari’anta masu adalci da masu mugunta, gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki, lokaci domin kowane abu.”
18 I said in my heart: "God tests people, so that they may see they're just animals." Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba.
19 Humans and animals share one fate: one dies as the other dies; both have the same breath. Humans have no advantage over animals—all is vapor. Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani.
20 All go to one place; all came from the dust, and all return to the dust. Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma.
21 Who knows whether the human spirit goes up, and whether the animal's spirit goes down to the earth? Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”
22 So I saw nothing is better than a person rejoicing in their work, since that is their lot. For who can show them what comes after them? Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa?
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]