Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Ecclesiastes 11 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Burodi a bisa ruwaye

1Ka jefa burodinka a bisa ruwaye,gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.

2Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas,gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.

3In gizagizai sun cika da ruwa,sukan zub da ruwan sama bisa duniya.Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa,inda ya fāɗi a nan zai kwanta.

4Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba,mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.

5Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba,ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya,haka ba za ka fahimci aikin AllahMahaliccin dukan abubuwa ba.

6Ka shuka irinka da safe,da yamma kuma kada ka janye hannunka,gama ba ka san wanda zai yi albarka ba,ko wannan ko wancan,ko kuma duka biyunsu su yi albarka.

Ka tuna da mahaliccinka a ƙuruciyarka

7Haske da yana da kyau,abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana.

8Kome tsawon rayuwar mutum,bari yă more su duka.Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu,gama su ma za su yi yawa.Duk abin da zai faru ba shi da amfani.

9Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.Ka bi shawarar zuciyarkada kuma duk abin da idanunka suka gani,amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nanAllah zai shari’anta ka.

10Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarkaka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka,gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]