Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Hosea 6 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Isra’ila marar tuba

1“Ku zo, mu koma ga Ubangiji.Ya yayyage mu kucu-kucuamma zai warkar da mu;ya ji mana ciwoamma zai daure mana miyakunmu.

2Bayan kwana biyu zai rayar da mu,a rana ta uku zai tashe mu,don mu rayu a gabansa.

3Bari mu yarda da Ubangiji;bari mu nace gaba don mu yarda da shi.Muddin rana tana fitowa,zai bayyana;zai zo mana kamar ruwan bazara,kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”

4“Me zan yi da kai Efraim?Me zan yi da kai Yahuda?Ƙaunarku tana kamar hazon safiya,kamar raɓar safiya da takan ɓace.

5Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana,na kashe ku da kalmomin bakina;hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.

6Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.

7Kamar Adamu, sun tā da alkawari,sun yi mini rashin aminci a can.

8Gileyad birni ce ta mugayen mutane,da tabon alamun jini.

9Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,haka ƙungiyoyin firistoci suke;suna kisa a hanya zuwa Shekem,suna aikata laifofi bankunya.

10Na ga wani abu mai bantsoroa gidan Isra’ila.A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanciIsra’ila kuma ta ƙazantu.

11“Ku kuma, ya mutanen Yahuda,na shirya muku ranar girbi.“A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]