Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 145 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda.

1Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;zan yabi sunanka har abada abadin.

2Kowace rana zan yabe kain kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.

3Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabogirmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.

4Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;za su yi magana game da manyan ayyukanka.

5Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja,zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.

6Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro,zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.

7Za su yi bikin yalwar alherinkasuka kuma rera adalcinka da farin ciki.

8Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.

9Ubangiji nagari ne ga duka;yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.

10Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji;tsarkakanka za su ɗaukaka ka.

11Za su yi maganar ɗaukakar mulkinkaza su kuma yi zancen ikonka,

12saboda dukan mutane su san manyan ayyukankada ɗaukakar darajar mulkinka.

13Mulkinka madawwamin mulki ne,sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai.Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransamai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.

14Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗiyana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.

15Idanun kowa yana dogara gare ka,kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.

16Ka buɗe hannunkaka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.

17Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsayana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.

18Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.

19Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa;yakan ji kukansu yă kuma cece su.

20Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa,amma dukan mugaye zai hallaka su.

21Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji.Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarkihar abada abadin.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]