Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Isaiah 35 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Farin cikin waɗanda aka ceta

1Hamada da ƙeƙasasshiyar ƙasa za su yi murna;jeji zai yi farin ciki ya kuma hudo.Kamar fure,

2zai buɗu ya hudo;zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki.Za a maido wa Lebanon da darajarta,darajar Karmel da Sharon;za su ga ɗaukakar Ubangiji,darajar Allahnmu.

3Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi,ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;

4ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata,“Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro;Allahnku zai zo,zai zo domin ya ɗau fansa;da ramuwar Allahzai zo don yă cece ku.”

5Sa’an nan idanun makafi za su buɗekunnuwan kurame kuma su ji.

6Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa,bebaye kuma su yi sowa don farin ciki.Ruwa zai kwararo daga jejirafuffuka kuma a cikin hamada.

7Yashi mai ƙuna zai zama tafki,ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka.A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama,ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.

8Kuma babbar hanya za tă kasance a can;za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki.Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba;za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce;mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.

9Zaki ba zai kasance a can ba,balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta;ba za a same su a can ba.Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,

10kuma fansassu na Ubangiji za su komo.Za su shiga Sihiyona da rerawa;matuƙar farin ciki zai mamaye su.Murna da farin ciki za su sha kansu,baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]