Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Hosea 11 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Ƙaunar Allah domin Isra’ila

1“Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi,daga Masar kuma na kira ɗana.

2Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ilahaka nesa da ni da suke ta yi.Suka miƙa hadaya ga Ba’alsuka kuma ƙona turare ga siffofi.

3Ni ne na koya wa Efraim tafiyaina kama su da hannu;amma ba su ganecewa ni ne na warkar da su ba.

4Na bishe su da linzamin alheri da tausayi,da ragamar ƙauna;Na cire karkiya daga wuyansuna kuma rusuna na ciyar da su.

5“Ba za su koma Masar baAssuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu basaboda sun ƙi su tuba ba?

6Takuba za su yi ta wulgawa a biranensu,za su hallaka sandunan ƙarafan ƙofofinsusu kuma kawo ƙarshen ƙulle-ƙullensu.

7Mutanena sun ƙudura su juye daga gare ni.Ko da ma suka yi kira ga Mafi Ɗaukaka,ta ko ƙaƙa ba zai girmama su ba.

8“Yaya zan ba da kai, Efraim?Yaya zan miƙa ka, Isra’ila?Yaya zan yi da kai kamar Adma?Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim?Zuciyata ta canja a cikina;dukan tausayina ya huru.

9Ba zan zartar da fushina mai zafi ba,ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba.Gama ni Allah ne, ba mutum ba,Mai Tsarki a cikinku.Ba zan zo cikin fushi ba.

10Za su bi Ubangiji;zai yi ruri kamar zaki.Sa’ad da ya yi ruri,’ya’yansa za su zo da rawan jiki daga yamma.

11Za su zo da rawan jikikamar tsuntsaye daga Masar,kamar kurciyoyi daga Assuriya.Zan zaunar da su a cikin gidajensu,”in ji Ubangiji.

Zunubin Isra’ila

12Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi,gidan Isra’ila da ruɗu.Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji,har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]