Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Isaiah 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The word that Isaiah son of Amoz saw concerning Judah and Jerusalem. Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.
2 In the last days the mountain of our Father's house will be firmly established as the highest of the mountains, raised above the hills, and all the nations will stream to it. A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.
3 Many peoples will come and say, "Come, let us go up to the mountain of God, to his house, so he can teach us his ways and we can walk in his paths." For instruction will go out from Zion, and the word of our Father from Jerusalem. Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima.
4 He will judge between the nations and settle disputes for many peoples. They will beat their swords into plowshares and their spears into pruning hooks; nation will not lift up sword against nation, nor will they train for war anymore. Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.
5 House of Jacob, come, let us walk in the light of our Father. Ki zo, ya gidan Yaƙub, bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.
6 For you have abandoned your people, the house of Jacob, because they are filled with influences from the east and with fortune-tellers like the Philistines, and they have made alliances with foreigners. Ka rabu da mutanenka, gidan Yaƙub. Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas; suna yin duba kamar Filistiyawa suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.
7 Their land is full of silver and gold, with no end to their treasures; their land is full of horses, with no end to their chariots. Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya; dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da dawakai; kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka.
8 Their land is full of idols; they bow down to the work of their hands, to what their own fingers have made. Ƙasarsu ta cika da gumaka; sukan rusuna ga aikin hannuwansu, ga abin da yatsotsinsu suka yi.
9 So mankind is brought low, and everyone is humbled—do not forgive them. Saboda an jawo mutum ƙasa aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam, kada ku gafarta musu.
10 Go into the rocks and hide in the dust from the dread of our Father and from the splendor of his majesty. Ku tafi cikin duwatsu, ku ɓuya cikin ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa!
11 The proud eyes of mankind will be brought low, and the arrogance of men will be humbled; our Father alone will be exalted in that day. Za a ƙasƙantar da mai girman kai za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.
12 For the Father of heaven's armies has a day in store against all that is proud and lofty, against all that is lifted up, so that it will be brought low, Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye domin dukan masu girman kai da masu fariya domin dukan waɗanda aka ɗaukaka (zai kuwa ƙasƙantar da su),
13 against all the cedars of Lebanon, lofty and lifted up, and against all the oaks of Bashan, domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya, da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,
14 against all the high mountains and against all the lofty hills, domin dukan dogayen duwatsu da kuma tuddai masu tsayi,
15 against every high tower and against every fortified wall, domin kowace doguwar hasumiya da kowace katanga mai ƙarfi,
16 against all the ships of Tarshish and against every magnificent vessel. domin kowane jirgin ruwan kasuwanci da kuma jirgi mafi girma mafi kyau.
17 The arrogance of mankind will be humbled, and the pride of men brought low; our Father alone will be exalted in that day, Za a jawo mai girman kai ƙasa a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,
18 and the idols will completely vanish. za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.
19 People will flee into the caves of the rocks and into holes in the ground from the dread of our Father and from the splendor of his majesty, when he rises to shake the earth. Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
20 In that day people will throw away their idols of silver and their idols of gold to the moles and bats, which they made for themselves to worship. A wannan rana mutane za su zubar wa jaba da jamage gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya da suka yi don su bauta musu.
21 They will go into the clefts of the rocks and into the crevices of the cliffs from the dread of our Father and from the splendor of his majesty, when he rises to shake the earth. Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma zuwa tsagaggun duwatsu daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
22 Stop trusting in mere man, who has only breath in his nostrils. What good is he? Ku daina dogara ga mutum, wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa. Wace daraja gare shi?
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]