Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Isaiah 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 For look—the Father of heaven's armies is about to strip from Jerusalem and from Judah every support and supply: the whole supply of bread and the whole supply of water, Yanzu ka duba fa, Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako daga Urushalima da Yahuda dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa,
2 the warrior and the soldier, the judge and the prophet, the fortune-teller and the elder, jarumi, da soja, alƙali da annabi masu duba da dattijo,
3 the commander of fifty and the man of rank, the counselor, the skilled craftsman, and the clever enchanter. shugaban sojojin hamsin da mutum mai makami, mai ba da shawara, gwanin sarrafa abubuwa da mai gwanintan dabo.
4 "I will make mere boys their officials, and childish whim will rule over them. “Zan sa ’yan yara su zama shugabanninsu; ’yan yara kurum za su yi mulkinsu.”
5 The people will oppress one another, each man against his neighbor; the young will rise up against the old, and the lowly against the honored." Mutane za su zalunci juna mutum da mutum, maƙwabci da maƙwabci. Yara za su rena tsofaffi, ƙasƙantacce zai rena mai daraja.
6 A man will seize his brother in his father's house and say, "You have a coat—you be our leader; take charge of this heap of ruins." Mutum zai kama ɗaya daga cikin ’yan’uwansa a gidan mahaifinsa ya ce, “Kana da abin sawa, ka zama shugabanmu; wannan kango kuma yă zama a ƙarƙashinka!”
7 But on that day he will cry out, "I am no healer! There is no bread and no coat in my house—you will not make me leader of the people." Amma a ranan nan zai tā da murya ya ce, “Ba ni ba dai. Ba ni da abinci ko abin sawa a gidana; kada ka mai da ni shugaban mutane.”
8 For Jerusalem has stumbled and Judah has fallen, because their words and their deeds are against our Father, defying his glorious presence. Urushalima tana tangaɗi, Yahuda yana fāɗuwa; maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji, suna rena ɗaukakar kasancewarsa.
9 The look on their faces testifies against them; they flaunt their sin like Sodom—they do not hide it. How terrible for them, for they have brought disaster on themselves! Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa.
10 Tell the righteous it will go well with them, for they will eat the fruit of their deeds. Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau, gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi.
11 How terrible for the wicked! It will go badly for him, for what his hands have done will be repaid to him. Kaiton masu mugunta! Masifa tana a kansu! Za a rama abin da hannuwansu suka yi.
12 My people—children are their oppressors, and women rule over them. My people, your guides lead you astray and have swallowed up the path you should walk. Matasa suna zalunta mutanena, mata suna mulki a bisansu. Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku; suna karkatar da ku daga hanya.
13 Our Father takes his stand to bring his case; he rises to judge the peoples. Ubangiji ya ɗauki mazauninsa a cikin ɗakin shari’a; ya tashi don yă shari’anta mutane.
14 Our Father enters into judgment with the elders and officials of his people: "It is you who have devoured the vineyard; the plunder of the poor is in your houses. Ubangiji yana shari’a da dattawa da kuma shugabannin mutanensa, “Ku ne kuka lalace gonar inabina; ganimar talakawa suna a gidajenku.
15 What do you mean by crushing my people and grinding the faces of the poor?" declares the Father of heaven's armies. Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena kuna gurgurje fuskokin talakawa?” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
16 Our Father said: "Because the daughters of Zion are proud—walking with outstretched necks and flirting eyes, mincing along with quick little steps, jingling the anklets on their feet, Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas.
17 therefore the Sovereign Father will strike the heads of the daughters of Zion with scabs, and our Father will lay bare their foreheads." Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona; Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.”
18 On that day the Sovereign Father will strip away their finery: the anklets, the headbands, the crescent ornaments, A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,
19 the earrings, the bracelets, the veils, ’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu,
20 the headdresses, the ankle chains, the sashes, the perfume flasks, the charms, kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu,
21 the signet rings, the nose rings, da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu,
22 the festival robes, the capes, the cloaks, the purses, tufafi masu kyau, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakar kuɗinsu
23 the hand mirrors, the fine linen garments, the turbans, and the shawls. da madubi, da kuma tufafin lilin da adikai, da gyale.
24 Then, instead of perfume there will be a stench; instead of a sash, a rope; instead of elegantly styled hair, baldness; instead of fine robes, a wrapping of coarse cloth; branding instead of beauty. A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji; a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu; a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai; a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki; a maimakon kyau, za su zama munana.
25 Your men will fall by the sword, your warriors in the battle. Mazanku za su mutu ta wurin takobi, jarumawanku za su mutu a yaƙi.
26 Her gates will mourn and lament; stripped bare, she will sit on the ground. Ƙofofin Sihiyona za su yi makoki su kuma yi kuka; za tă zama wofi, za tă zauna a ƙasa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]