Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Amos 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Hear this word our Father has spoken against you, children of Israel—against the whole family I brought up from Egypt: Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.
2 Of all the families of the earth, I have known only you; therefore I will hold you accountable for all your sins. “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.”
3 Do two walk together, unless they have agreed to meet? Mutum biyu za su iya yin tafiya tare in ba su yarda su yi haka ba?
4 Does a lion roar in the forest when he has no prey? Does a young lion cry out from his den if he has caught nothing? Zaki yakan yi ruri a jeji in bai sami kama nama ba? Zai yi gurnani a cikin kogonsa in bai kama kome ba?
5 Does a bird fall into a snare on the ground when there is no trap for it? Does a snare spring up from the earth when it has caught nothing? Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa inda ba a sa tarko ba, ko tarko yakan zargu daga ƙasa in ba abin da ya taɓa shi?
6 If a ram's horn is blown in a city, will the people not tremble? If disaster comes to a city, has our Father not done it? Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?
7 Surely the Sovereign Father does nothing without revealing his secret to his servants the prophets. Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
8 The lion has roared—who will not fear? The Sovereign Father has spoken—who can keep from prophesying? Zaki ya yi ruri, wa ba zai tsorata ba? Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana, wa ba zai yi annabci ba?
9 Proclaim over the strongholds in Ashdod and over the strongholds in the land of Egypt, and say: "Assemble on the mountains of Samaria and see the great uproar within her, and the oppression in her midst." Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”
10 They do not know how to do right, declares our Father—those who hoard up violence and plunder in their strongholds. “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”
11 So the Sovereign Father says: An enemy will surround the land, topple your defenses, and loot your strongholds. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.”
12 This is what our Father says: As a shepherd rescues two legs or a piece of an ear from the lion's mouth, so the children of Israel living in Samaria will be rescued—with a corner of a couch, part of a bed. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”
13 Hear, and testify against the house of Jacob, declares the Sovereign Father, the Father of heaven's armies: “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.
14 On the day I punish Israel for his rebellions, I will also punish the altars of Bethel; the horns of the altar will be cut off and fall to the ground. “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa
15 I will strike the winter house along with the summer house; the houses of ivory will perish, and the great houses will come to an end, declares our Father. Zan rushe gidan rani da na damina; gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” in ji Ubangiji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]