Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Amos 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 This is what our Father says: For three sins of Moab, and for four, I will not revoke it—he burned the bones of Edom's king to lime. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Mowab, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom suka zama sai ka ce toka.
2 So I will send fire on Moab, and it will devour the strongholds of Kerioth; Moab will die amid the uproar, with shouting and the sound of the shofar. Zan sa wuta a Mowab da za tă ƙone kagarun Keriyot Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.
3 I will cut off the ruler from her midst and kill all her officials with him, says our Father. Zan hallaka mai mulkinta zan kuma kashe shugabanninta.”
4 This is what our Father says: For three sins of Judah, and for four, I will not revoke it—they rejected our Father's instruction and did not keep his rules, and their lies led them astray, the same lies their ancestors followed. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Yahuda, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, domin allolin ƙarya sun ruɗe su, allolin da kakanninsu suka bauta.
5 So I will send fire on Judah, and it will devour the strongholds of Jerusalem. Zan sa wuta a Yahuda da za tă ƙone kagarun Urushalima.”
6 This is what our Father says: For three sins of Israel, and four, I won't relent—they sell the righteous for silver, the needy for a pair of sandals. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.
7 They trample the heads of the poor into the dust of the earth and push the afflicted off the road. A man and his father go to the same girl, profaning my holy name. Sun tattake kawunan matalauta kamar yadda suke taka laka suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya. Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda, suna kuma ɓata sunana mai tsarki.
8 They stretch out beside every altar on garments taken as collateral, and in the house of their God they drink the wine of those they have fined. Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade a kan tufafin da suka karɓe jingina. A gidajen allolinsu sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
9 Yet it was I who destroyed the Amorite before them, as tall as the cedars and as strong as the oaks; I destroyed his fruit above and his roots below. “Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
10 And it was I who brought you up out of the land of Egypt and led you forty years in the wilderness, to take possession of the land of the Amorite. Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa.
11 I raised up some of your sons as prophets and some of your young men as Nazirites. Is this not so, people of Israel? declares our Father. “Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji.
12 But you made the Nazirites drink wine, and you commanded the prophets, saying, "Do not prophesy." “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.
13 Look, I will crush you in your place, as a cart full of sheaves crushes the ground beneath it. “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.
14 Even the swift will find no escape, the strong will not hold on to his strength, and the warrior will not save his life. Masu gudu da sauri ba za su tsira ba, masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba, jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.
15 The archer will not stand his ground, the fleet-footed will not escape, and the horseman will not save his life. ’Yan baka ba za su iya dāgewa ba, masu saurin gudu ba za su tsira ba mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.
16 Even the bravest of the warriors will flee away naked on that day, declares our Father. Ko jarumawa mafi jaruntaka za su gudu tsirara a ranan nan,” in ji Ubangiji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]