Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Amos 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The words of Amos, a shepherd of Tekoa, which he saw about Israel when Uzziah ruled Judah and Jeroboam son of Joash ruled Israel, two years before the earthquake. Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.
2 He said: Our Father roars from Zion, sounds his voice from Jerusalem; the shepherds' pastures mourn, and Carmel's summit withers. Ya ce, “Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”
3 This is what our Father says: For three sins of Damascus, and for four, I will not turn it back, because they threshed Gilead with sledges of iron. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Damaskus, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Domin sun ci zalunci Gileyad zalunci mai tsanani,
4 So I will send a fire upon the house of Hazael, and it will devour the strongholds of Ben-hadad. zan sa wuta a gidan Hazayel, da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad.
5 I will break the gate-bar of Damascus, and cut off the one who sits enthroned in the Valley of Aven and the one who holds the scepter in Beth-eden; and the people of Aram will go into exile to Kir, says our Father. Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus; zan hallaka sarkin da yake cikin Kwarin Awen da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden. Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,” in ji Ubangiji.
6 So says our Father: For three crimes of Gaza, and for four, I will not reverse it—they exiled an entire people, handing them over to Edom. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Gaza, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun sayar wa Edom,
7 So I will send a fire upon the wall of Gaza, and it will devour her strongholds. Zan aika da wuta a katangar Gaza ta ƙone duk kagarunta.
8 I will cut off the one enthroned in Ashdod and the one who holds the scepter in Ashkelon; I will turn my hand against Ekron, and the remnant of the Philistines will perish, says the Sovereign Father. Zan hallaka sarkin Ashdod da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. Zan hukunta Ekron, har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9 So says our Father: For three sins of Tyre, and for four, I will not relent, because they handed over a whole community of exiles to Edom and forgot the covenant of brothers. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,
10 So I will send a fire upon the wall of Tyre, and it will devour her strongholds. zan aika da wuta a Taya, da za tă ƙone kagarunta.”
11 This is what our Father says: For three sins of Edom, and for four, I will not relent, because he chased his brother with the sword, stifled all compassion, his anger tore endlessly, and he kept his wrath forever. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba.
12 So I will send a fire upon Teman, and it will devour the strongholds of Bozrah. Zan aika wuta a Teman da za tă ƙone kagarun Bozra.”
13 This is what our Father says: For three sins of the Ammonites, and for four, I will not relent, because they ripped open Gilead's pregnant women to enlarge their border. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.
14 So I will kindle a fire on the wall of Rabbah, and it will devour her strongholds, with shouting on the day of battle, with a tempest on the day of the whirlwind. Zan sa wuta a katangar Rabba da za tă ƙone kagarunta za a yi kururuwa a ranar yaƙi, faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.
15 And their king will go into exile, he and his officials together, says our Father. Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]