Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 26 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Ta Dawuda.

1Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji,gama na yi rayuwa marar zargi;Na dogara ga Ubangijiba tare da kaucewa ba.

2Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni,ka bincike zuciyata da tunanina;

3gama ƙaunarka kullum tana a gabana,kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.

4Ba na zama tare da masu ruɗu,ko in yi tarayya da masu riya;

5na ƙi jinin taron masu aikata muguntana ƙi in zauna tare da mugaye.

6Na wanke hannuwana cikin rashin laifi,ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,

7ina shelar yabonka da ƙarfiina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.

8Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji,wurin da ɗaukakarka ke zaune.

9Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubiraina tare da masu son yin kisankai

10waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu,waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.

11Amma na yi rayuwa marar zargi;ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.

12Ƙafafuna suna tsaye daram;cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]