Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

James 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My brothers and sisters, as believers in our glorious Lord Jesus Christ, do not show favoritism. ’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.
2 Say a man wearing a gold ring and fine clothes enters your assembly, and a poor man in shabby clothes enters too. A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo,
3 If you notice the well-dressed one and say, "Sit here, a good seat," but tell the poor man, "Stand over there," or "Sit on the floor by my feet," in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”
4 haven't you played favorites among yourselves and become judges guided by evil motives? ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?
5 Listen, my beloved brothers and sisters: Hasn't our Father chosen the world's poor to be rich in faith, heirs of the kingdom promised to those who love him? Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
6 But you disrespected the poor. Don't the rich oppress you and drag you into court? Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?
7 Aren't they blaspheming the honorable name called over you? Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?
8 If you truly obey the royal law according to the Scripture, "Love your neighbor as yourself," you do well. In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.
9 But if you show favoritism, you are sinning, and the law convicts you as lawbreakers. Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.
10 Whoever keeps the whole law but stumbles at one point is guilty of breaking it all. Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.
11 For our Father, who forbade adultery, also forbade murder. So if you avoid adultery yet commit murder, you're a lawbreaker. Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.
12 Speak and act as people who will be judged by the law of freedom. Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci,
13 Judgment is merciless to one who showed no mercy; mercy triumphs over judgment. gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!
14 What good is it, my brothers and sisters, if someone claims faith without works? Can that faith save him? Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa?
15 Suppose a brother or sister is poorly clothed and lacking daily food, A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini,
16 and one of you tells them, "Go in peace, stay warm and fed," but gives nothing for their bodily needs—what good is that? sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani?
17 In the same way, faith by itself, if it is not accompanied by works, is dead. Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.
18 But someone will say, "You have faith, and I have works." Show me your faith without works, and I'll show you my faith from my works. Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.” Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi.
19 You believe that our Father is one; you do well. Even the demons believe that—and shudder. Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.
20 Do you want me to show you, you foolish person, that faith apart from works is useless? Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?
21 Was not Abraham our father justified by works when he offered his son Isaac on the altar? Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade?
22 You see that faith was working together with his works, and faith was completed by his works. Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi.
23 This fulfilled the Scripture: "Abraham believed our Father, and it was credited to him as righteousness"—he was called our Father's friend. Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.
24 You see that a person is justified by works and not by faith alone. Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.
25 Likewise, wasn't Rahab the prostitute also justified by works, welcoming the messengers and sending them out a different way? Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam?
26 As the body without the spirit is dead, so also faith without works is dead. Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]