Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

James 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My brothers and sisters, not many of you should become teachers, since we teachers face stricter judgment. Kada yawancinku su so ɗaukan kansu a matsayin malamai, ’yan’uwana, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shari’a mafi tsanani.
2 For we all stumble in many ways. Anyone who never stumbles in speech is a mature man, able to control his whole body too. Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.
3 If we put bits in horses' mouths to make them obey us, we guide their whole bodies too. Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya.
4 Consider ships too: though large and driven by strong winds, a tiny rudder steers them wherever the pilot wants. Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so.
5 So too the tongue is a small body part, yet boasts great things. See how small a fire sets ablaze a great forest! Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana.
6 The tongue is a fire, a world of wickedness placed among our body's parts. It stains the whole body, sets the whole course of life ablaze, and is itself set ablaze by hell. Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.
7 Every kind of beast, bird, reptile, and sea creature is tamed, and has been tamed, by humankind, Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa,
8 but no human being can tame the tongue. It is a restless evil, full of deadly poison. amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.
9 With it we bless our Father; with it we curse people made in the likeness of our Father. Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah.
10 From the same mouth come blessing and cursing. My brothers and sisters, this should not be. Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba.
11 Does a spring pour out both fresh and bitter water from the same opening? Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya?
12 Brothers and sisters, can a fig tree bear olives, or a vine figs? Neither can a salt spring yield fresh water. ’Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar ’ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi yă haifi ’ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.
13 Who is wise and understanding among you? Let him show his deeds through good conduct, in wisdom's humility. Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.
14 But if bitter envy and selfish ambition fill your heart, don't boast or lie against the truth. Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya.
15 This is not the wisdom that comes down from above, but is earthly, unspiritual, demonic. Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma.
16 For where there is jealousy and selfish ambition, there will be disorder and every vile practice. Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.
17 Wisdom from above: pure first, then peace-loving, gentle, reasonable, full of mercy and good fruit, unbiased, sincere. Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.
18 And the harvest of righteousness is sown in peace by those who make peace. Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]