Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

James 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 James, a servant of our Father and the Lord Jesus Christ, to the twelve tribes scattered among the nations: greetings. Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin al’ummai. Gaisuwa mai yawa.
2 Consider it pure joy, my brothers and sisters, whenever you face trials of many kinds, Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku,
3 because you know that the testing of your faith produces perseverance. domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa.
4 Let perseverance finish its work so that you may be mature and complete, lacking nothing. Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
5 If any of you lacks wisdom, ask our Father, who gives freely to all without criticizing, and it will be given you. In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.
6 Ask in faith, without doubting, for the doubter is like a sea wave, driven and tossed by the wind. Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.
7 That person should not expect to receive anything from our Father. Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji;
8 Such a person is double-minded and unstable in all their ways. shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.
9 Let the believer in humble circumstances take pride in their high position, Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka.
10 but let the rich boast in their low state, since they'll pass like a wildflower. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji.
11 The sun rises with scorching heat and withers the grass. Its flower falls; its beauty vanishes. So the rich fade away amid their pursuits. Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.
12 Blessed is the one who endures trial, because once tested they'll receive the crown of life our Father promised to those who love him. Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
13 When tempted, no one should say, "Our Father is tempting me." Evil can't tempt our Father, and he tempts no one. Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa;
14 But each person is tempted, dragged away and lured by their own evil desire. amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi.
15 Then desire conceives and gives birth to sin; sin, full-grown, gives birth to death. Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.
16 Don't be deceived, my dear brothers and sisters. Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu.
17 Every good and perfect gift is from above, coming down from the Father of lights, who never changes or casts a shifting shadow. Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
18 By his choice, he gave us birth through the word of truth, so we'd be a kind of firstfruits of his creation. Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta.
19 Know this, my dear brothers and sisters: everyone should be quick to listen, slow to speak, slow to anger, ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,
20 because human anger does not produce the righteousness of our Father. gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.
21 So strip off all moral filth and excess evil; humbly receive the word planted in you, able to save your souls. Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku.
22 Do not merely listen to the word, and so deceive yourselves. Do what it says. Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.
23 Anyone who hears the word but doesn't act on it is like one who looks at his natural face in a mirror, Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi
24 and, after looking at himself, goes away and immediately forgets what he looks like. bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa.
25 But whoever peers into the perfect law of freedom, continuing in it—not a forgetful hearer but a doer who acts—will be blessed in his doing. Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.
26 If anyone thinks himself religious but doesn't control his tongue, he deceives his own heart—his religion is worthless. In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.
27 Pure and spotless religion before our Father is this: caring for orphans and widows in their distress, and keeping oneself unstained from the world. Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]