Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Job 35 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

1Sai Elihu ya ce,

2“Ko kana tsammani wannan gaskiya ne?Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’

3Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita,kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’

4“Zan so in ba ka amsakai tare da abokanka.

5Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani;ku dubi gizagizai a samanku.

6In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah?In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?

7In kuna da adalci, me kuka ba shi,ko kuma me ya karɓa daga hannunku?

8Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai,adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai.

9“Mutane suna kuka don yawan zalunci;suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi.

10Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni,mai ba da waƙoƙi cikin dare,

11wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniyaya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’

12Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimakodomin girman kan mugaye.

13Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi;Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.

14Ta yaya zai saurara sosai ko zai sauraralokacin da kake cewa ba ka ganinsa,cewa ka kawo ƙara a wurinsakuma dole ka jira shi.

15Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsako kaɗan ba ya kula da mugunta.

16Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai;yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]