Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Job 18 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Bildad

1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

2“Yaushe za ka gama maganganun nan?Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.

3Don me muke kamar shanu a wurinka,ka ɗauke mu mutanen wofi?

4Kai da ka yayyage kanka don haushi,za a yashe duniya saboda kai ne?Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?

5“An kashe fitilar mugu;harshen wutarsa ya daina ci.

6Wutar cikin tentinsa ta zama duhu;fitilar da take kusa da shi ta mutu.

7Ƙarfin takawarsa ya ragu;dabararsa ta ja fāɗuwarsa.

8Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga,yana ta yawo a cikin ragar.

9Tarko ya kama ɗiɗɗigensa;tarko ya riƙe shi kam.

10An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa;an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.

11Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefeyana bin shi duk inda ya je.

12Masifa tana jiransa;bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.

13Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa;ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.

14An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsaaka sa shi tsoro sosai.

15Wuta ta cinye tentinsa;farar wuta ta rufe wurin da yake zama.

16Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasarassansa sun mutu a sama.

17An manta da shi a duniya;ba wanda yake ƙara tunawa da shi.

18An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu,an kore shi daga duniya.

19Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa,ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.

20Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi;tsoro ya kama mutanen gabas.

21Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake,haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]