Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Leviticus 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "If someone's offering is a peace offering from the herd, male or female, he must present it without defect before me. “ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce, ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji.
2 He lays his hand on his offering's head and slaughters it at the tent of meeting's entrance, and Aaron's sons the priests splash the blood against all sides of the altar. Yă kuma ɗibiya hannunsa bisa kan hadayarsa, yă yanka ta a mashigin Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna waɗanda suke firistoci za su yayyafa jinin a kan bagade a kowane gefe.
3 From the peace offering he must present to me a food offering made by fire: the fat covering the inner parts and all the fat on them, Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su,
4 both kidneys with the fat on them near the flanks, and the long lobe of the liver, which he removes with the kidneys. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
5 Aaron's sons will burn it on the altar atop the burnt offering on the wood over the fire—a food offering, a pleasing aroma to me. ’Ya’yan Haruna za su ƙone shi a kan bagade a bisa hadaya ta ƙonawa wadda take a kan itacen da yake cin wuta, kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
6 "If his peace offering to me is from the flock, male or female, he must present it without defect. “ ‘In ya miƙa dabba ce daga garke a matsayin hadaya ta salama ga Ubangiji, zai miƙa namiji ko ta mace marar lahani.
7 If he brings a lamb as his offering, he is to present it before me, In ya miƙa ɗan rago ne, zai kawo shi a gaban Ubangiji.
8 lay his hand on the head of his offering and slaughter it before the tent of meeting; Aaron's sons will splash its blood on all sides of the altar. Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade.
9 From the peace offering he must present a food offering to me by fire: its fat, the whole fat tail cut off close to the backbone, the fat covering the inner parts, and all the fat on them, Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su,
10 both kidneys with the fat near the loins, and the liver's long lobe, which he removes with the kidneys. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
11 The priest will burn it on the altar as food, an offering made to me by fire. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar hadayar abinci, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
12 "If his offering is a goat, he is to present it before me, “ ‘In yana miƙa akuya ce, zai kawo ta a gaban Ubangiji.
13 lay his hand on its head and slaughter it in front of the tent of meeting; Aaron's sons will splash its blood on all sides of the altar. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jininta a kowane gefe na bagade.
14 From it he must present a food offering to me by fire: the fat covering the inner parts and all the fat on them, Daga abin da zai miƙa sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, dukan kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,
15 both kidneys with their fat near the loins, and the liver's long lobe, which he removes with the kidneys. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
16 The priest will burn them on the altar as food, an offering by fire, a pleasing aroma. All fat is mine. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar abinci, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi. Dukan kitsen na Ubangiji ne.
17 "This is a lasting rule for all generations, wherever you live: never eat any fat or any blood." “ ‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’ ”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]