Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Leviticus 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "When anyone brings a grain offering to our Father, the offering must be fine flour. Pour oil on it, put frankincense on it, “ ‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa
2 and bring it to Aaron's sons, the priests. The priest will take a handful of its fine flour and oil, with all its frankincense, and burn the memorial portion on the altar—a fire offering, a pleasing aroma to our Father. yă kai wa ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
3 The rest of the grain offering belongs to Aaron and his sons—most holy, from the fire offerings to our Father. Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta.
4 "When you bring a grain offering baked in an oven: fine flour, either loaves without yeast mixed with oil, or wafers without yeast spread with oil. “ ‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai.
5 If your offering is a grain offering on a griddle, it must be fine flour mixed with oil, without yeast. In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba.
6 Break it into pieces and pour oil on it; it is a grain offering. A gutsuttsura shi, a zuba mai a kansa, hadaya ce ta hatsi.
7 If your offering is grain cooked in a pan, make it with fine flour and oil. In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai.
8 Bring the grain offering made from these to our Father; present it to the priest, who brings it to the altar. A kawo hatsin da aka yi da waɗannan abubuwa ga Ubangiji; a ba wa firist wanda zai ɗauka yă kai bagade.
9 The priest takes the grain offering's memorial portion and burns it on the altar—a fire offering, a pleasing aroma to our Father. Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
10 What remains of the grain offering belongs to Aaron and his sons—most holy, from the fire offerings to our Father. Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta.
11 "No grain offering you bring to our Father may contain yeast, for you must not burn any yeast or honey as a fire offering to our Father. “ ‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba.
12 You may bring them to our Father as a firstfruits offering, but do not offer them on the altar as a pleasing aroma. Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba.
13 Salt every grain offering. Don't leave out your Father's covenant salt; add salt to all your offerings. A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.
14 "If you bring a firstfruits grain offering to our Father, offer new grain roasted in fire, crushed kernels, as your firstfruits offering. “ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta.
15 Put oil on it and lay frankincense on it; it is a grain offering. A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi.
16 The priest burns the memorial portion—some of the crushed grain and oil—with all its frankincense, as a fire offering to our Father." Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]