Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Leviticus 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father called to Moses and spoke to him from the tent of meeting, saying: Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce,
2 "Speak to the Israelites and say to them: When any of you brings me an offering, bring your offering of livestock from the herd or the flock. “Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku.
3 "If his offering is a burnt offering from the herd, he is to offer a male without defect, offering it at the entrance of the tent of meeting, to be accepted before me. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji.
4 He is to lay his hand on the burnt offering's head, and it will be accepted for him, to atone for him. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa.
5 He is to kill the young bull before me, and Aaron's sons the priests are to bring the blood and splash it around the altar at the entrance of the tent of meeting. Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da ’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada.
6 Then he is to skin the burnt offering and cut it into its pieces. Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa.
7 Aaron's sons the priests will lay a fire on the altar and arrange wood on it. ’Ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su hura wuta a bagade, su kuma shirya itace a kan wutar.
8 Aaron's sons, the priests, arrange the pieces, head, and fat on the wood over the fire on the altar. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden.
9 He is to wash its inner organs and legs with water; the priest burns it all on the altar—a burnt offering, a food offering, a pleasing aroma to me. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
10 "If his burnt offering is from the flock—sheep or goats—he must bring a male without defect. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga garke ne, ko na tumaki, ko na awaki, zai miƙa namiji ne marar lahani.
11 He is to slaughter it on the altar's north side before me; Aaron's sons the priests are to splash its blood around the altar. Zai yanka shi a gefen arewa na bagaden a gaban Ubangiji, ’ya’yan Haruna firistoci kuwa za su yayyafa jinin dabbar a bagaden a kowane gefe.
12 He is to cut it into pieces—head and fat—and the priest is to arrange them on the wood, on the fire, on the altar. Zai yanka shi gunduwa-gunduwa, firist kuwa zai shirya su haɗe da kan, da kuma kitsen a kan itace mai cin wutar da yake a kan bagade.
13 He must wash the inner organs and legs with water; the priest offers it all, burns it on the altar—a burnt offering, a food offering, a pleasing aroma to me. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
14 "If his burnt offering to me is a bird, he must bring turtledoves or young pigeons as his offering. “ ‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko ’yar tattabara.
15 The priest brings it to the altar, wrings off its head, burns it there; its blood drains against the altar's side. Firist zai kawo ta bagade, yă murɗe wuyan tsuntsun yă ƙone shi a kan bagade; zai tsiyaye jininsa tsuntsun a gefen bagaden.
16 He removes its crop with its contents, throwing it beside the altar eastward, at the ash heap. Amma zai ɗauki kayan cikin tsuntsun da gashin yă zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka.
17 He is to tear it open by the wings, not fully apart; the priest will burn it on the altar's wood over the fire—a burnt offering, a food offering, a pleasing aroma to me." Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, yă ƙone shi. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]