Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Leviticus 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father spoke to Moses, saying: Ubangiji ya ce wa Musa,
2 "Tell the Israelites: If a person sins unintentionally against any of our Father's commands, doing what must not be done, and breaks one of them, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,
3 if the anointed priest sins, bringing guilt on the people, he must bring our Father a young bull without defect as a sin offering for the sin he committed. “ ‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi.
4 He is to bring the bull to the tent of meeting's entrance before our Father, lay his hand on its head, and slaughter it before our Father. Zai kawo bijimin a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan bijimin, yă kuma yanka shi a gaban Ubangiji.
5 The anointed priest takes some of the bull's blood and brings it into the tent of meeting. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗiba jinin bijimin yă kai cikin Tentin Sujada.
6 He is to dip his finger in the blood, sprinkling it seven times before our Father in front of the sanctuary veil. Yă tsoma yatsarsa a cikin jinin, yă kuma yafa sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen wuri mai tsarki.
7 The priest is to put some of the blood on the horns of the altar of fragrant incense before our Father, which is in the tent of meeting, and pour all the rest of the bull's blood at the base of the burnt-offering altar at the entrance of the tent of meeting. Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
8 He is to remove all the fat of the sin offering bull: the fat covering the entrails, and all the fat on the entrails. Zai cire dukan kitsen daga bijimin hadaya don zunubi, kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,
9 The two kidneys, the fat on them near the loins, and the liver's lobe—he removes with the kidneys, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta, waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
10 as removed from the ox of the peace offering; the priest is to burn them on the altar of burnt offering. Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin yă ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya.
11 But the bull's hide, all its flesh, head, legs, intestines, and dung. Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa,
12 He must carry all the rest of the bull outside the camp to a clean place where ashes are dumped, and burn it on a wood fire; it must be burned where ashes are dumped. wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka.
13 "If Israel's whole congregation sins unintentionally, and the matter is hidden from the assembly's eyes, and they do one of the things our Father commanded not to be done, and become guilty. “ ‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi.
14 When the sin they committed becomes known, the assembly must offer a young bull as a sin offering and bring it before the tent of meeting. Sa’ad da suka gane da zunubin da suka aikata, dole taron su kawo ɗan bijimi a matsayin hadaya don zunubi, su kawo shi a gaban Tentin Sujada.
15 The elders of the community lay hands on the bull's head before our Father; then it is slaughtered before our Father. Dattawan jama’a za su ɗibiya hannuwansu a kan bijimin a gaban Ubangiji, sai a yanka bijimin a gaban Ubangiji.
16 Then the anointed priest is to bring some of the bull's blood into the tent of meeting. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗibi jinin bijimi zuwa cikin Tentin Sujada.
17 He is to dip his finger in the blood and sprinkle seven times before our Father, in front of the veil. Zai tsoma yatsarsa cikin jini yă kuma yayyafa shi a gaban Ubangiji sau bakwai a gaban labule.
18 He is to put some of the blood on the altar's horns before our Father in the tent of meeting, then pour all the rest of it at the base of the altar of burnt offering, at the tent of meeting's entrance. Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
19 He is to remove all its fat and burn it on the altar. Zai cire dukan kitsen daga gare shi yă ƙone a kan bagade,
20 He is to do the same with this bull as with the sin offering's bull. So the priest will atone for them, and they'll be forgiven. yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu.
21 He is to carry the bull outside the camp and burn it as he burned the first bull; it is the assembly's sin offering. Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a.
22 "When a leader sins, unintentionally doing anything our Father commanded not to do, and becomes guilty, “ ‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi.
23 if he learns of the sin he committed, he must bring as his offering a male goat without defect. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa.
24 He is to lay his hand on the goat's head and slaughter it where the burnt offering is slaughtered before our Father—a sin offering. Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi.
25 The priest will take some sin-offering blood with his finger, and put it on the burnt-offering altar's horns, then pour the rest at its base. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
26 He is to burn all its fat on the altar, like the fat of the peace offering. The priest will atone for his sin, and he will be forgiven. Zai ƙone dukan kitse a kan bagade kamar yadda ya ƙone kitsen hadaya ta salama. Ta haka firist zai yi kafara saboda zunubin mutumin, za a kuwa gafarta masa.
27 "If anyone of the common people sins unintentionally, doing any one of the things our Father commanded not to do, and incurs guilt, “ ‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.
28 when he becomes aware of his sin, he must bring a female goat without defect as his offering for the sin he committed. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi.
29 He is to lay his hand on the sin offering's head and slaughter it at the burnt offering's place. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.
30 With his finger the priest puts some of its blood on the burnt-offering altar's horns, then pours all the rest at its base. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade.
31 He is to remove all its fat, as fat is removed from the peace offering; the priest is to burn it on the altar—a pleasing aroma to our Father—and make atonement for him, and he will be forgiven. Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.
32 "If he brings a lamb as his sin offering, he is to bring a female without defect. “ ‘Idan kuwa daga cikin ’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ’yar tunkiya marar lahani.
33 He is to lay his hand on the sin offering's head and slaughter it as a sin offering where the burnt offering is slaughtered. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa.
34 With his finger the priest is to take some of the blood from the sin offering and apply it to the horns of the altar where burnt offerings are made, then pour out all the remaining blood at the altar's base. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
35 He must remove all its fat, as the lamb's fat is removed from the peace offering; the priest will burn it on the altar atop the fire offerings to our Father. So the priest will atone for him for the sin he committed, and he will be forgiven." Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]