Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Leviticus 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "If anyone sins by hearing a public call to testify, and is a witness, having seen or known, yet stays silent, he bears his guilt. “ ‘Mutum zai yi zunubi in bai yi magana ba sa’ad da ya ji ana shelar neman shaida game da wani abin da ya gani ko kuwa ya ji, alhakin zai zauna a wuyansa.
2 "Or if someone unknowingly touches any unclean thing, or a carcass—unclean wild animal, unclean livestock, or unclean swarming creature—he becomes unclean and guilty. “ ‘Ko kuwa in mutum ya taɓa wani abin da yake mai ƙazanta, ko gawar naman jeji marar tsabta, ko na shanu marar tsabta, ko na halittu marasa tsabtan da suke motsi a ƙasa; ko da yake bai sani ba, ya ƙazantu ke nan, kuma ya yi laifi.
3 "Or if he touches human impurity—any impurity that makes one unclean—unknowingly, then learns of it, he is guilty. Ko kuwa in ya taɓa rashin tsabta na mutane, wani abin da zai sa shi rashin tsabta; ko da yake bai sani ba, sa’ad da ya gane, zai zama mai laifi.
4 "Or if anyone rashly swears an oath to do evil or good—whatever people rashly swear—and it's hidden from him, when he realizes it, he's guilty in any of these. Ko kuwa in mutum bai yi tunani ba, ya yi rantsuwar yin wani abu, ko mai kyau ko marar kyau; ko da yake bai sani ba, duk da haka sa’ad da ya gane zai zama mai laifi.
5 When anyone is guilty in any of these matters, he must confess the sin he has committed. Sa’ad da wani yana da laifi a kowanne cikin waɗannan hanyoyi, dole yă furta a hanyar da ya yi zunubin
6 He must bring our Father a penalty offering for the sin he committed—a female from the flock, a lamb or goat—as a sin offering; the priest will atone for his sin. kuma don zunubin da ya yi, dole yă kawo wa Ubangiji tunkiya ko akuya daga garke kamar hadaya don zunubi; firist kuwa zai yi kafara dominsa da kuma domin zunubinsa.
7 "If he can't afford a lamb, he must bring our Father two turtledoves or two young pigeons as penalty for his sin—one as a sin offering, the other as a burnt offering. “ ‘In ba zai iya kawo tunkiyar ba, sai yă kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ga Ubangiji a matsayin hakki don zunubinsa, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa.
8 He brings them to the priest, who presents the sin offering first, wringing its head at the neck without separating it. Zai kawo su wa firist, wanda da fari zai miƙa ɗaya domin hadaya don zunubi. Zai murɗe kan daga wuyanta, ba tare da tsinke kan gaba ɗaya ba,
9 He sprinkles some blood from the sin offering on the altar's side; the rest drains at its base. It is a sin offering. zai kuma yayyafa jinin hadaya don zunubin a gefen bagade; a tsiyaye sauran jinin kuma a gindin bagade. Hadaya ce ta zunubi.
10 The second bird he offers as a burnt offering, per the rule. The priest atones for his sin, and he is forgiven. Firist zai miƙa ɗayan matsayin hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka tsara, yă kuma yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.
11 "But if he cannot afford two doves or two young pigeons, he must bring two quarts of fine flour as his sin offering—no oil or incense on it, for it is a sin offering. “ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi.
12 He must bring it to the priest, who takes a handful as its memorial portion and burns it on the altar atop our Father's fire offerings. It is a sin offering. Zai kawo wa firist, firist kuwa zai ɗiba da hannu don yă kasance abin tunawa, sai yă ƙone a bisan bagaden kamar hadayar da ake ƙona da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi.
13 The priest will atone for him for any of these sins he committed, and he'll be forgiven; the rest belongs to the priest, like the grain offering." Ta haka firist zai yi kafara dominsa saboda dukan waɗannan zunuban da ya yi, za a kuwa gafarta masa. Sauran hadayar za tă zama ta firist, kamar yadda yake bisa ga hadaya ta gari.’ ”
14 Then our Father said to Moses, Ubangiji ya ce wa Musa,
15 "If anyone is unfaithful and sins unintentionally against any of our Father's holy things, he must bring our Father a ram without defect from the flock as his guilt offering, valued in silver by weight by the sanctuary standard—a guilt offering. “Sa’ad da mutum ya ci amana, ya kuma yi zunubi ba da gangan ba dangane da wani cikin abubuwa masu tsarki na Ubangiji, zai kawo ga Ubangiji rago daga garke wanda ba shi da lahani saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimata kuɗinsa bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Hadaya ce ta laifi.
16 He must repay for the holy thing he sinned against, adding a fifth, and give it to the priest. The priest will atone for him with the guilt-offering ram, and he'll be forgiven. Dole yă biya abin da ya kāsa yi dangane da abubuwa masu tsarki, yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar abin a kan wannan sa’an nan yă ba wa firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa.
17 "If anyone sins, doing what our Father commanded not to be done, even unknowingly, he is guilty and bears his wrongdoing. “In mutum ya yi zunubi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake bai sani ba, shi mai laifi ne. Za a kuwa nemi hakki daga gare shi.
18 He must bring the priest a flawless ram from the flock, at the assessed value, as a guilt offering; the priest will atone for his unwitting sin, and he'll be forgiven. Zai kawo wa firist rago daga garke, marar lahani. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa.
19 It is a guilt offering; he was certainly guilty before our Father." Hadaya ce ta laifi, ya yi laifi na abin da ya yi marar kyau ga Ubangiji.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]