Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Leviticus 6 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
2 "If anyone sins, unfaithful to your Father, by deceiving his neighbor about a deposit, a pledge, or stolen goods, or by cheating him, “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin,
3 or if he finds lost property and lies about it, swearing falsely—any such act by which a person sins. ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi,
4 When he sins and is guilty, he must return what he stole, or extorted, or the deposit entrusted to him, or the lost item he found, sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.
5 or whatever he swore falsely about, he must repay it in full, add a fifth to it, and give it to its owner on the day he admits his guilt. Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.
6 He must bring his guilt offering to your Father: a ram without defect from the flock, at your valuation, as a guilt offering, to the priest. A matsayin hakki kuwa, dole yă kawo wa firist, wato, ga Ubangiji, hadaya rago marar lahani kuma wanda aka kimanta tamaninsa daga garke don laifinsa.
7 The priest will atone for him before your Father, and he'll be forgiven for whatever he did that made him guilty." Ta haka firist zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.”
8 Then our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
9 "Command Aaron and his sons: This is the law for the burnt offering. It stays on the altar's hearth all night until morning, and the altar fire must keep burning on it. “Ka ba Haruna da ’ya’yansa maza wannan umarni, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za tă kasance a bagade dukan dare, sai da safe, kuma dole a bar wutar tă yi ta ci a bisa bagaden.
10 The priest is to wear his linen garment, with linen undergarments against his skin, then remove the ashes left after the fire consumes the burnt offering on the altar, and place them beside the altar. Sa’an nan firist zai sa rigunarsa ta lilin da kuma rigar lilin da ake sa a ciki, sa’an nan yă kwashe tokan hadaya ta ƙonawa da wuta da ta ci a kan bagaden, yă sa kusa da bagaden.
11 Then he removes his garments, puts on others, and carries the ashes outside the camp to a clean place. Sa’an nan yă tuɓe waɗannan rigunan yă sa waɗansu, sa’an nan yă ɗauki tokar yă kai waje da sansani zuwa inda yake da tsabta.
12 The altar fire must keep burning; it must not go out. Every morning the priest adds wood on it, arranges the burnt offering on it, and burns the fat of the peace offerings on it. Dole a bar wutar da take bisa bagaden tă yi ta ci; kada tă mutu. Kowace safiya firist zai ƙara itacen wuta, yă shirya hadaya ta ƙonawa a bisa wutar yă kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a kansa.
13 The fire must be kept burning on the altar continually; it must not go out. Dole a bar wutar tă ci gaba da ci a bisa bagade; kada tă mutu.
14 "This is the law of the grain offering: Aaron's sons must bring it before your Father, in front of the altar. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya ta gari. ’Ya’yan Haruna za su kawo ta a gaban Ubangiji, a gaban bagaden.
15 The priest takes a handful of the grain offering's fine flour and oil, with all its frankincense, and burns this memorial portion on the altar as a pleasing aroma to your Father. Firist zai ɗiba garin hadayar mai laushin wanda aka zuba masa mai da kuma turare cike da tafin hannu. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.
16 Aaron and his sons eat what remains; it must be eaten without yeast in a holy place, eaten in the courtyard of the tent of meeting. Haruna da ’ya’yansa maza za su ci sauran, amma za a ci shi ba tare da yisti ba a tsattsarkan wuri; za su ci shi a harabar Tentin Sujada.
17 Do not bake it with yeast. I've given it as their share of my food offerings, like the sin and guilt offerings; it is most holy. Ba za a toya shi da yisti ba; na ba su yă zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.
18 Every male of Aaron's descendants may eat it—a lasting portion through your generations from your Father's food offerings. Whatever touches them becomes holy." Kowane ɗa namiji cikin zuriyar Haruna zai iya cinsa. Wannan rabonsa ne na kullum na hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk abin da ya taɓa hadayun zai tsarkaka.’ ”
19 Our Father said to Moses: Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
20 "This is Aaron and his sons' offering to your Father on the day he is anointed: about two quarts of fine flour as a regular grain offering, half in the morning, half in the evening. “Wannan ne hadayar da Haruna da ’ya’yansa maza za su kawo ga Ubangiji a ranar da za a naɗa su firistoci, humushin garwan gari mai laushi a matsayin hadaya ta gari na kullum, rabinsa da safe, rabinsa kuma da yamma.
21 Prepare it with oil on a griddle, bring it well-kneaded, present the grain offering in broken pieces—a pleasing aroma to your Father. A shirya shi da mai a kwanon tuya, a kawo shi kwaɓaɓɓe sosai, a miƙa shi hadaya ta gari dunƙule-dunƙule don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
22 The anointed priest who succeeds him from among his sons must prepare it—a lasting decree before your Father: it must be burned completely. Duk wanda aka naɗa daga ’ya’yan Haruna yă zama firist a madadinsa, shi ne zai miƙa wannan hadayar ga Ubangiji. Zai ƙone hadayar ƙurmus. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce har abada.
23 Every grain offering of a priest is to be burned completely; it must not be eaten." Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ƙurmus, ba za a ci ba.”
24 Again our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
25 "Tell Aaron and his sons: this is the law of the sin offering: slaughter it before your Father, where the burnt offering is slaughtered; it is most holy. “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya don zunubi. Za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji a inda ake yankan hadaya ta ƙonawa; dole tă kasance mai tsarki.
26 The priest who offers it for sin must eat it; it must be eaten in a holy place, in the tent of meeting's courtyard. Firist da ya miƙa ta zai ci, za a ci ta a tsattsarkan wuri, a harabar Tentin Sujada.
27 Whatever touches its flesh becomes holy. If its blood spatters a garment, wash the spattered spot in a holy place. Duk abin da ya taɓa wani sashe na naman, zai zama da tsarki, kuma in wani jini ya ɗiga a riga, dole ka wanke shi a tsattsarkan wuri.
28 The clay pot it is boiled in must be broken; if boiled in a bronze pot, it must be scoured and rinsed with water. Dole a farfashe tukunyar lakar da aka dafa naman a ciki; amma in an dafa a tukunyar tagulla, sai a kankare tukunyar, a kuma ɗauraye da ruwa.
29 Every male among the priests may eat it; it is most holy. Kowane namiji a iyalin firistoci zai iya ci; gama abu ne mafi tsarki.
30 No sin offering whose blood is brought into the tent of meeting to atone in the Holy Place may be eaten; it must be burned with fire." Amma duk wata hadaya don zunubi wadda aka kawo jininta cikin Tentin Sujada don a yi kafara a Wuri Mai Tsarki, ba za a ci ba. A maimako haka za a ƙone ta ɗungum.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]