Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Leviticus 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "This is the law of the guilt offering. It is most holy. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi na hadaya don laifi, hadaya ce tsattsarka.
2 Where they slaughter the burnt offering, they must slaughter the guilt offering; splatter its blood on all sides of the altar. Za a yanka hadaya don laifi a inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, za a kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagade.
3 All its fat is offered: the fat tail and fat covering the inner organs, Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki,
4 the two kidneys and their fat at the loins, and the liver's long lobe, removed with the kidneys. da ƙodoji biyu da kitsen da yake a bisansu kusa da kwiɓi, da kuma rufin hanta, wanda za a cire tare da ƙodoji.
5 The priest burns them on the altar as a food offering to our Father; a guilt offering. Firist zai ƙone su a kan bagade, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce don laifi.
6 Any male priest may eat it, eaten only in a holy place; it is most holy. Kowane da namiji cikin iyalin firistoci zai iya ci. Sai a tsattsarkan wuri ne za a ci; gama abu mafi tsarki ne.
7 "The sin offering and guilt offering share one law: it belongs to the priest who makes atonement with it. “ ‘Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ƙa’ida hanyar yinsu iri ɗaya ce. Su ɗin na firist da ya yi kafara da su ne.
8 The priest who offers anyone's burnt offering keeps its hide for himself. Firist da ya miƙa hadaya ta ƙonawa domin wani, zai iya ajiye fatar wa kansa.
9 Any grain offering baked in an oven, and all made in a pan or on a griddle, belongs to the priest who offers it. Kowace hadaya ta garin da aka toya a tanda, ko aka dafa a tukunya ko a kan kaskon tuya, na firist da ya miƙa ta ne,
10 Every grain offering, mixed with oil or dry, belongs equally to all Aaron's sons. kuma kowace hadaya ta gari wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, ita ma, ta dukan ’ya’ya Haruna ne maza.
11 "This is the law of the sacrifice of peace offerings that anyone may bring to our Father. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodin hadaya don zumuncin da mutum zai iya miƙa ga Ubangiji.
12 If he presents it as a thank offering, with it he must offer unleavened cakes mixed with oil, unleavened wafers coated with oil, and cakes of fine flour well kneaded and mixed with oil. “ ‘In ya miƙa hadayar a matsayin hadaya ta godiya ce, to, zai miƙa ta tare da burodi mai kauri marar yisti, wanda aka kwaɓa da mai, da burodi marar kauri, wanda aka shafa wa mai, da kuma burodi mai kauri da aka yi da gari mai laushi wanda aka kwaɓa sosai da mai.
13 He must bring loaves of leavened bread with his thanksgiving sacrifice of peace offerings. Tare da hadayarsa don zumunci ta godiya, zai miƙa dunƙulen burodin da aka yi da yisti.
14 From it he must give one of each as a contribution to our Father; it belongs to the priest who spatters the blood of the peace offerings. Zai kuma kawo ɗaya daga kowace a matsayin hadaya, baiko ne ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist da ya yafa jinin hadaya ta salama ne.
15 The meat of his thanksgiving peace offerings must be eaten the day it's offered; none of it may remain until morning. Za a ci wannan nama na hadaya don zumunci ta godiya a ranar da aka miƙa ta, kada yă bar wani abu daga naman yă kwana.
16 "If his offering is a vow or voluntary sacrifice, it must be eaten the day he offers it; what remains may be eaten the next day. “ ‘In hadayarsa cika wa’adin rantsuwa ce ko kuwa ta yardar rai ce, sai a ci hadayar a ranar da ya miƙa ta, amma za a iya cin duk abin da ya rage kashegari.
17 But any sacrifice flesh remaining on the third day must be burned in fire. Duk naman hadayar da ya rage har kwana uku, dole a ƙone shi.
18 If any of his peace offering's meat is eaten on the third day, it won't be accepted, it won't count for the offerer—it's tainted, and whoever eats it bears his guilt. Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami albarkar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci kuwa ya yi laifi.
19 "Flesh that touches anything unclean must not be eaten—burn that flesh in fire. But other flesh: anyone clean may eat it. “ ‘Ba za a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki ba; dole a ƙone shi. Game da sauran nama, kowa da yake mai tsarki zai iya ci.
20 Anyone who eats meat of our Father's peace offering while unclean will be cut off from his people. Amma in wani wanda ba shi da tsarki ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa.
21 Whoever touches anything unclean—human impurity, an unclean animal, or any unclean, detestable thing—then eats meat from our Father's peace offering, that person will be cut off from his people." Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa.’ ”
22 Our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
23 "Tell the people of Israel: Do not eat any fat from ox, sheep, or goat. “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Kada ku ci wani kitsen shanu, ko na tumaki, ko kuwa na awaki.
24 Fat from a carcass or animal mauled by a predator may serve any purpose, but never eat it. Za a iya yin wani amfani da kitsen dabbar da ta mutu mushe, ko kitsen dabbar da namun jeji su yayyaga, amma kada a kuskura a ci.
25 Anyone who eats fat from an animal offered to me by fire will be cut off from his people. Duk wanda ya ci kitsen dabbar da aka miƙa ta wuta ga Ubangiji, za a fid da shi daga mutanensa.
26 You must not eat any blood at all, from bird or animal, wherever you live. Kuma duk inda kuke zama, ba za ku ci jinin wani tsuntsu ko na dabba ba.
27 Anyone who eats any blood will be cut off from his people." Duk wanda ya ci jini, za a fid da mutumin daga mutanensa.’ ”
28 Our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
29 "Speak to the Israelites: Whoever presents his peace offering to me must bring his offering to me from that sacrifice. “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Duk wanda ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.
30 With his hands he must bring my food offerings; the fat with the breast he must bring, to wave the breast as a wave offering before me. Da hannuwansa zai kawo hadayar da za a ƙona ga Ubangiji; zai kawo kitsen tare da ƙirjin, yă kuma kaɗa ƙirjin a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.
31 The priest burns the fat on the altar; the breast belongs to Aaron and his sons. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagade, amma ƙirjin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza.
32 You are to give the right thigh to the priest as a contribution from your peace offerings. Za ku ba da cinya ta dama ta hadaya don zumuncinku ga firist a matsayin baiko.
33 Whichever son of Aaron offers the peace offering's blood and fat gets the right thigh as his portion. Ɗan Haruna da ya miƙa jini da kitsen hadaya ta salama, zai ɗauki cinyar tă zama rabonsa.
34 For I have taken the breast of the wave offering and thigh of the contribution from Israel's peace offerings, and given them to Aaron the priest and his sons as a permanent share from Israel." Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ”
35 This is Aaron and his sons' portion from our Father's food offerings, from the day they were presented to serve our Father as priests. Wannan shi ne sashen hadayar da aka ba wa Haruna da ’ya’yansa maza, hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta, tun ranar da aka gabatar da su don su yi wa Ubangiji hidima a matsayin firist.
36 Our Father commanded this be given them from the Israelites, the day he anointed them—a permanent share for all their generations. A ranar da aka keɓe su, Ubangiji ya umarta cewa Isra’ilawa su ba da wannan a gare su a matsayin rabonsu na kullum, a dukan tsararraki masu zuwa.
37 This is the law for burnt offerings, grain offerings, sin offerings, guilt offerings, ordination offerings, and peace offerings, Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, hadaya don zunubi, hadaya don laifi, hadaya ta naɗi da kuma hadaya ta salama,
38 which our Father commanded Moses on Mount Sinai, the day he commanded the people of Israel to bring their offerings to our Father in the Wilderness of Sinai. waɗanda Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai, a Hamadar Sinai, a ranar da ya umarci Isra’ilawa su kawo hadayunsu ga Ubangiji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]