Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Lamentations 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 How the Sovereign Father in his anger has shrouded daughter Zion in a cloud! He has hurled down from heaven to earth the splendor of Israel; he has not remembered his footstool in the day of his anger. Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona da gizagizan fushi! Ya jefar da darajar Isra’ila daga sama zuwa ƙasa; bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba a ranar fushinsa.
2 The Sovereign Father has swallowed up without mercy all the dwellings of Jacob; in his wrath he has torn down the strongholds of daughter Judah. He has brought down to the ground in dishonor her kingdom and its rulers. Ubangiji ya hallakar da wurin zaman Yaƙub ba tausayi; A cikin fushinsa kuma zai rurrushe kagaran Diyar Yahuda. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulki.
3 In fierce anger he has stripped Israel of all her strength; he has withdrawn his right hand and left them exposed to the enemy. He has burned in Jacob like a flaming fire that consumes on every side. A cikin zafin fushi ya fasa kowane ƙaho na Isra’ila. Ya janye hannun damansa sa’ad da maƙiyi ya zo. Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone duk abin da yake kusa da ita.
4 He has bent his bow like an enemy, his right hand poised like a foe; and he has killed all who were lovely to see. In the tent of daughter Zion he has poured out his fury like fire. Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa; hannun damansa na shirye. Kamar maƙiyi, ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani; ya zuba fushinsa kamar wuta a kan tenti na Diyar Sihiyona.
5 The Sovereign Father has become like an enemy; he has swallowed up Israel. He has swallowed up all her palaces and laid in ruins her strongholds, and he has heaped mourning and lamentation on daughter Judah. Ubangiji kamar maƙiyi ne; ya hallaka Isra’ila. Ya hallaka wurarenta duka ya kuma hallaka kagaranta. Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki wa Diyar Yahuda.
6 He has stripped his shelter like a garden, he has ruined his appointed place. Our Father has made Zion forget appointed feast and sabbath, and in his fierce anger he has spurned king and priest. Ya rushe haikalinsa kamar lambu; ya hallaka wurin yi masa sujada. Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci; a cikin zafin fushinsa ya watsar da sarki da firist.
7 The Sovereign Father has rejected his altar, disowned his sanctuary; he has handed over to the enemy the walls of her palaces. They raised a shout in the house of our Father as on a day of festival. Ubangiji ya ƙi bagadensa ya kuma yi wofi da haikalinsa. Ya ba maƙiyinta fadodinta; suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji kamar a ranar da ake yin biki.
8 Our Father determined to lay in ruins the wall of daughter Zion. He stretched out the measuring line; he did not hold back his hand from destroying. He made rampart and wall lament; together they fell to ruin. Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon da yake kewaye da Diyar Sihiyona. Ya auna da igiyar awo bai fasa hallaka ta ba. Ya sa katanga da katanga duk suka lalace.
9 Her gates have sunk into the ground; he has ruined and broken her bars. Her king and her princes are among the nations; the law is no more, and her prophets find no vision from our Father. Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa; ya kakkarya ƙarafanta. Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe, babu sauran doka, annabawa kuma ba su samun wahayi daga wurin Ubangiji.
10 The elders of daughter Zion sit on the ground in silence; they have thrown dust on their heads and put on mourning clothes. The young women of Jerusalem have bowed their heads to the ground. Dattawan Diyar Sihiyona sun zauna shiru a ƙasa; suka kuma sa rigar buhu. ’Yan matan Urushalima suka sunkuyar da kawunansu ƙasa.
11 My eyes are worn out from weeping; my stomach churns; my heart is poured out on the ground because of the destruction of the daughter of my people, as children and infants faint in the streets of the city. Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni.
12 They cry to their mothers, "Where is bread and wine?" as they faint like the wounded in the streets of the city, as their life is poured out in their mothers' arms. Suna ce wa uwayensu, “Ina burodi da ruwan inabi?” Yayinda suke suma kamar mutanen da aka ji masu ciwo a cikin birni, sa’ad da suke mutuwa a hannuwan uwayensu.
13 What can I say for you, to what can I compare you, daughter Jerusalem? What can I liken to you, that I may comfort you, virgin daughter Zion? For your ruin is vast as the sea; who can heal you? Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ke Diyar Urushalima? Da me zan misalta ki, yadda zan iya yi miki ta’aziyya, Ke Budurwa Diyar Sihiyona? Ciwonki yana da zurfi kamar teku. Wane ne zai iya warkar da ke?
14 Your prophets have seen for you false and deceptive visions; they did not expose your guilt to restore your fortunes, but have seen for you oracles that are false and misleading. Wahayin annabawanki ƙarya ne kuma marasa amfani; ba su tona zunubanki ba yadda za su iya ceto ki daga bauta ba. Sun yi miki annabcin ƙarya marar amfani.
15 All who pass by clap their hands at you; they hiss and shake their heads at daughter Jerusalem: "Is this the city that was called the perfection of beauty, the joy of all the earth?" Duk masu wucewa suna yi miki tafi na reni; suna yi wa Diyar Urushalima tsaki suna kaɗa kai suna cewa, “Wannan ne birnin da aka ce kyakkyawa ne, mai farantawa dukan duniya rai?”
16 All your enemies open their mouths against you; they hiss and gnash their teeth and cry, "We have swallowed her! This is the day we longed for; we have found it, we have seen it!" Maƙiyanki duka suna ta surutu game da ke; suna tsaki suna cizon haƙora suna cewa, “Mun hallaka ta. Wannan ce ranar da muke jira; yau mun gan ta.”
17 Our Father has done what he purposed; he has carried out his word which he commanded long ago. He has torn down without pity; he has let the enemy gloat over you and raised up the power of your foes. Ubangiji ya yi abin da ya shirya; ya cika maganarsa, wadda ya umarta tun daɗewa. Ya jefar da ke ba tausayi, ya bari maƙiya sun yi nasara da ke, ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.
18 The people's heart cried out to the Sovereign Father. Wall of daughter Zion, let tears stream down like a torrent day and night! Give yourself no rest, your eyes no relief. Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta.
19 Arise, cry out in the night at the start of each night watch! Pour out your heart like water before the Sovereign Father! Lift your hands to him for the lives of your children, who faint from hunger at every street corner. Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi.
20 Look, our Father, and consider: whom have you ever treated like this? Should women eat their offspring, the children they have cradled? Should priest and prophet be killed in the sanctuary of the Sovereign Father? “Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji?
21 Young and old lie on the ground in the streets; my young women and my young men have fallen by the sword. You have killed them in the day of your anger, slaughtering without pity. “Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi.
22 You summoned, as to a festival day, terrors on every side; and on the day of our Father's anger no one escaped or survived. My enemy has destroyed those I cradled and raised. “Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]