Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Lamentations 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 I am the man who has seen affliction under the rod of his wrath. Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji.
2 He has driven me away and made me walk in darkness without any light. Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske;
3 Surely against me he turns his hand again and again, all day long. ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini.
4 He has worn away my flesh and my skin; he has broken my bones. Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana.
5 He has besieged me and surrounded me with bitterness and hardship. Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala.
6 He has made me dwell in darkness like those long dead. Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa.
7 He has walled me in so I cannot escape; he has weighed down my chains. Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.
8 Even when I call out and cry for help, he shuts out my prayer. Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.
9 He has blocked my ways with cut stones; he has made my paths crooked. Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace.
10 He is a bear lying in wait for me, a lion in hiding. Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye,
11 He drove me off my path and tore me to pieces; he has made me desolate. ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako.
12 He bent his bow and set me as the target for his arrow. Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa.
13 He drove the arrows of his quiver into my vitals. Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.
14 I have become the laughingstock of all my people, their mocking song all day long. Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.
15 He has filled me with bitterness; he has sated me with bitterness. Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci.
16 He has made my teeth grind on gravel, and made me cower in the dust. Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura.
17 My soul has lost all peace; I have forgotten what happiness is. An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.
18 So I say, "My endurance has perished, and so has my hope from our Father." Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
19 Remember my affliction and my wandering, the bitterness and the gall! Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.
20 My soul continually remembers it and is bowed down within me. Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.
21 But this I call to mind, and therefore I have hope: Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba.
22 The covenant love of our Father never ceases; his mercies never come to an end; Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 they are new every morning; great is your faithfulness. Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne.
24 "Our Father is all I need," says my soul, "therefore I will hope in him." Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.”
25 Our Father is good to those who wait for him, to the soul who seeks him. Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;
26 It is good to wait quietly for the salvation of our Father. yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.
27 It is good for a man to bear the yoke in his youth. Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.
28 Let him sit alone in silence when it is laid on him; Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.
29 let him put his mouth in the dust—there may yet be hope; Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.
30 let him give his cheek to the one who strikes, and be filled with insults. Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.
31 For the Sovereign Father will not abandon forever. Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada.
32 Though he causes grief, he will have compassion according to the abundance of his covenant love; Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.
33 for he does not willingly afflict or grieve people. Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.
34 To crush underfoot all the prisoners of the earth, Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba,
35 to deny a man justice in the sight of the Most High, ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki,
36 to deprive a man of justice in his case—the Sovereign Father does not approve. ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
37 Who has spoken and it came to pass, unless the Sovereign Father has commanded it? Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba?
38 Is it not from the mouth of the Most High that both calamity and good come? Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?
39 Why should a living man complain about the punishment for his sins? Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
40 Let us examine and test our ways, and return to our Father! Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.
41 Let us lift up our hearts and our hands to our Father in heaven: Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce,
42 "We have sinned and rebelled, and you have not forgiven. “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba.
43 You have wrapped yourself in anger and pursued us, killing without pity; “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi.
44 you have wrapped yourself with a cloud so that no prayer can pass through. Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka.
45 You have made us scum and refuse among the peoples. Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane.
46 All our enemies open their mouths against us; “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi.
47 panic and pitfall have come upon us, devastation and destruction." Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”
48 My eyes flow with streams of water over the destruction of my people. Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.
49 My eyes will flow without ceasing, without respite, Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.
50 until our Father looks down and sees from heaven. Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.
51 My eyes bring grief to my soul at the fate of all the daughters of my city. Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.
52 I have been hunted like a bird by those who were my enemies without cause; Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu.
53 they flung me alive into a pit and cast stones on me; Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu;
54 water closed over my head; I said, "I am lost." ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
55 I called on your name, my Father, from the depths of the pit; Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.
56 you heard my plea: "Do not turn a deaf ear to my cry for help!" Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”
57 You came near on the day I called on you; you said, "Do not fear!" Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”
58 You have taken up my cause, Sovereign Father; you have redeemed my life. Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.
59 You have seen the wrong done to me, my Father; judge my cause. Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!
60 You have seen all their vengeance, all their plots against me. Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini.
61 You have heard their taunts, my Father, all their plots against me, Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini
62 the lips and thoughts of my assailants against me all day long. Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini.
63 Watch their every move; I am the object of their mocking song. Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.
64 You will repay them, my Father, according to the work of their hands. Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi.
65 You will give them hardness of heart; your curse will be on them. Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su.
66 You will pursue them in anger and destroy them from under the heavens of our Father. Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]