Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Jonah 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Then the word of our Father came to Jonah a second time: Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu.
2 "Get up, go to Nineveh, that great city, and proclaim the message I give you." “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”
3 So Jonah got up and went to Nineveh, as our Father had said. Nineveh was a huge city—three days to cross. Sai Yunana ya yi biyayya da maganar Ubangiji, ya tafi Ninebe. Ninebe birni ne da yake da muhimmanci, wanda sai an ɗauki kwana uku kafin a iya zaga shi.
4 Jonah walked one day into the city and cried out, "Forty more days and Nineveh is overturned!" A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?”
5 The people of Nineveh believed God. They called a fast and put on sackcloth, from the greatest to the least. Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.
6 When the news reached Nineveh's king, he rose from his throne, removed his robe, covered himself with sackcloth, and sat in ashes. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.
7 He had this proclaimed in Nineveh, by decree of the king and his nobles: No person or animal, herd or flock, may taste anything; they must not graze or drink water. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha.
8 Let people and animals be covered with sackcloth, and everyone cry out to God with all their strength. Let each turn from his evil way and the violence in his hands. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.
9 Who knows? God may turn and change his mind, turn from his fierce anger, so we're not destroyed. Wa ya sani? Ko Allah zai ji tausayinmu da kuma juyayinmu yă janye zafin fushinsa don kada mu hallaka.”
10 When God saw their deeds—that they turned from their evil way—God changed his mind about the disaster he had threatened to bring on them, and did not do it. Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]