Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Jonah 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 But this upset Jonah deeply, and he burned with anger. Sai abin ya ɓata wa Yunana rai ƙwarai har ya yi fushi.
2 He prayed to our Father, "Please, O Father, isn't this what I said while still in my own land? That's why I fled toward Tarshish first—I knew you are a gracious, compassionate Father, slow to anger, overflowing with covenant love, one who relents from sending disaster. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci.
3 Now, our Father, please take my life from me—death is better for me than life." Yanzu, ya Ubangiji, ka ɗauki raina, domin ya fi sauƙi a gare ni in mutu da in rayu.”
4 And our Father said, "Is it right for you to be so angry?" Amma Ubangiji ya amsa, ya ce; “Daidai ne ka yi fushi?”
5 Jonah left the city and sat east of it, made himself a shelter there, and sat under it in the shade, waiting to see what would happen to the city. Sai Yunana ya fita daga birnin ya yi wajen gabas, ya zauna. A nan ya yi wa kansa rumfa, ya zauna cikin inuwarta yana jira yă ga abin da zai sami birnin.
6 And our Father appointed a plant and made it grow up over Jonah, to shade his head and ease his discomfort. So Jonah was overjoyed because of the plant. Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa.
7 At dawn the next day, our Father appointed a worm that attacked the plant, and it withered. Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu.
8 When the sun rose, our Father sent a scorching east wind; the sun beat on Jonah's head until he grew faint. He begged to die: "Better for me to die than to live." Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”
9 But our Father asked Jonah, "Is it right for you to be angry about the plant?" He said, "It is right—angry enough to die." Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?” Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.”
10 And our Father said, "You pitied the plant you did not work for or grow, which sprouted in a night and died in a night. Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita.
11 And should I not pity Nineveh, that great city, in which there are more than 120,000 people who cannot tell their right hand from their left, and many animals as well?" Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]