Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Joel 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Blow the ram's horn in Zion; sound the alarm on my holy mountain! Let all who live in the land tremble, for the day of our Father is coming—it is near: Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona; ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki. Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki, gama ranar Ubangiji tana zuwa. Tana gab da faruwa
2 A day of darkness and gloom, a day of clouds and thick darkness. Like dawn spreading across the mountains, a great and mighty army comes—nothing like it has ever been before, and nothing like it will ever come again. rana ce ta baƙin duhu ƙirin, ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa kamar ketowar alfijir a kan duwatsu yadda ba a taɓa ganin irinta ba, ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa.
3 Before them fire devours, and behind them a flame blazes. The land before them is like the garden of Eden, but behind them a desolate wilderness—and nothing escapes them. A gabansu wuta tana ci, a bayansu ga harshen wuta yana ci, A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden, a bayansu kuma jeji ne wofi, babu abin da ya kuɓuce musu.
4 They look like horses; like war horses they charge. Suna da kamannin dawakai; suna gudu kamar dokin yaƙi.
5 Like the rumbling of chariots they leap over the mountaintops, like the crackling of flame consuming stubble, like a mighty army drawn up for battle. Da motsi kamar na kekunan yaƙi sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu, kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka, kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi.
6 Before them peoples writhe in anguish; every face grows pale. Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba; kowace fuska ta yanƙwane.
7 Like warriors they charge; like soldiers they scale the wall. Each marches in line, never swerving from its course. Sukan auka kamar jarumawa; sukan hau katanga kamar sojoji. Kowa yana takawa bisa ga tsari, ba mai kaucewa.
8 They do not jostle one another; each keeps to its own path. They burst through the weapons and are not halted. Ba sa turin juna, kowane yakan miƙe gaba. Sukan kutsa cikin abokan gāba ba mai tsai da su.
9 They rush upon the city; they run along the wall. They climb into the houses; through the windows they enter like a thief. Sukan ruga cikin birni, suna gudu a kan katanga. Sukan hau gidaje, sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi.
10 Before them the earth quakes, the heavens tremble. The sun and moon grow dark, and the stars no longer shine. A gabansu duniya takan girgiza, sararin sama kuma yakan jijjigu, rana da wata su yi duhu, taurari kuma ba sa ba da haske.
11 Our Father raises his voice at the head of his army; his camp is very great, and mighty are those who carry out his word. The day of our Father is great and utterly terrifying—who can endure it? Ubangiji ya yi tsawa wa shugaban mayaƙansa; sojojinsa sun fi a ƙirge masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa. Ranar Ubangiji da girma take; mai banrazana. Wa zai iya jure mata?
12 "Yet even now," declares our Father, "return to me with all your heart, with fasting, with weeping, and with mourning. “Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.”
13 "Tear your hearts, not your garments. Return to your Father, for he is gracious and compassionate, slow to anger and abounding in covenant love, and he relents from sending disaster. Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i.
14 Who knows? He may turn and relent and leave behind a blessing—a grain offering and a drink offering for your Father." Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi yă sa mana albarka ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha wa Ubangiji Allahnku.
15 Blow a shofar in Zion; consecrate a fast; call a sacred assembly. A busa ƙaho a Sihiyona, a yi shelar azumi mai tsarki, a kira tsarkakan taro.
16 Gather the people; consecrate the assembly; bring together the elders; gather the children, even the infants nursing at the breast. Let the bridegroom come out of his room, and the bride from her chamber. A tattara mutane; ku tsarkake taron; ku kawo dattawa wuri ɗaya; ku kuma tara yara, da waɗanda suke shan mama. Bari ango yă bar ɗakinsa amarya kuma lolokinta.
17 Let the priests who minister before our Father weep between the portico and the altar. Let them say, "Spare your people, our Father, and do not make your inheritance an object of scorn, a byword among the nations. Why should they say among the peoples, 'Where is their God?'" Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji, su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji. Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, da abin ba’a a cikin al’ummai. Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”
18 Then our Father became jealous for his land and took pity on his people. Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa yă kuma ji tausayin mutanensa.
19 Our Father answered his people: "Look, I am sending you grain, new wine, and oil, and you will be satisfied with them. Never again will I make you an object of scorn among the nations." Ubangiji zai amsa musu ya ce, “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai, isashe da zai ƙosar da ku sosai; ba kuma zan ƙara maishe ku abin dariya ga al’ummai ba.
20 "I will drive the northern army far from you, pushing it into a parched and desolate land—its front ranks into the Dead Sea and its rear into the Mediterranean Sea. Its stench will rise; its foul smell will go up, for it has done monstrous things. “Zan kori sojojin arewa nesa da ku, in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma, kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum. Warinsu kuma zai bazu; ɗoyinsu zai tashi.” Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.
21 Don't be afraid, land; rejoice and be glad, for our Father has done great things! Kada ki ji tsoro, ya ƙasa; ki yi murna ki kuma yi farin ciki. Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.
22 Do not be afraid, you animals of the field, for the pastures of the wilderness are turning green; the tree bears its fruit; the fig tree and the vine yield their riches. Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji, gama wuraren kiwo sun yi kore shar. Itatuwa suna ba da ’ya’yansu; itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.
23 Be glad, children of Zion, and rejoice in your Father, for he has given you the autumn rain to show his faithfulness; he sends down for you abundant showers, the autumn and the spring rains, as before. Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona, ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku, gama ya ba ku ruwan bazara cikin adalci. Yakan aika muku yayyafi a yalwace, na bazara da na kaka, kamar dā.
24 The threshing floors will be full of grain; the vats will overflow with new wine and oil. Masussukai za su cika da hatsi; randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.
25 I will repay you for the years the locusts have eaten—the swarming locust, the young locust, the destroying locust, and the cutting locust—my great army that I sent among you. “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa, da kuma sauran fāra da tarin fāra babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.
26 You will eat your fill and be satisfied, and you will praise the name of your Father, who has dealt wondrously with you; and never again will my people be put to shame. Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi, za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku, wanda ya yi muku ayyukan banmamaki; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
27 Then you will know that I am in the midst of Israel, and that I am your Father, and there is no other; and never again will my people be put to shame. Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila, cewa ni ne Ubangiji Allahnku, babu wani kuma; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
28 "And afterward, I will pour out my Spirit on all flesh. Your sons and your daughters will prophesy, your old men will dream dreams, your young men will see visions. “Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi.
29 Even on the male servants and the female servants in those days I will pour out my Spirit. Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.
30 I will show wonders in the heavens and on the earth—blood and fire and columns of smoke. Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai da kuma a kan duniya, za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi.
31 The sun will be turned to darkness and the moon to blood before the great and awesome day of our Father comes." Rana za tă duhunta wata kuma yă zama jini kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.
32 And this will happen: everyone who calls on the name of the Lord will be saved; for on Mount Zion and in Jerusalem there will be deliverance, as our Father has said, among the survivors whom our Father calls. Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]