Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Joel 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The word of our Father that came to Joel son of Pethuel. Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.
2 Hear this, you elders; listen, all who live in this land. Has anything like this happened in your days, or in the days of your ancestors? Ku ji wannan, ku dattawa, ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar. Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin kakanninku?
3 Tell your children about it, and let your children tell their children, and their children the next generation. Ku faɗa wa ’ya’yanku, bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu, ’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.
4 What the cutting locust spared, the swarming locust ate; what the swarming locust spared, the hopping locust ate; and what the hopping locust spared, the destroying locust ate. Abin da ɗango ya bari fāri masu girma sun cinye; abin da fāri masu girma suka bari, burduduwa ta cinye; abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.
5 Wake up, you drunkards, and weep; wail, all you wine drinkers, over the sweet wine, for it has been cut off from your lips. Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka! Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi; ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi, gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.
6 "For a nation has invaded my land, mighty and beyond number; its teeth are the teeth of a lion, and it has the fangs of a lioness. Wata al’umma ta mamaye ƙasata, tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa; tana da haƙoran zaki, da zagar zakanya.
7 It has devastated my vines and splintered my fig tree; it has stripped off their bark and cast it aside, leaving their branches bare and white." Ta mayar da kuringar inabina kango ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena. Ta ɓamɓare bayansu duka ta kuma jefar da su ta bar rassansu fari fat.
8 Wail like a virgin dressed in mourning clothes for the husband of her youth. Ku yi makoki kamar budurwa a cikin tsummoki tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.
9 The grain offering and the drink offering are cut off from the house of our Father; the priests, the ministers of our Father, mourn. Hadayun hatsi da hadayun sha an yanke su daga gidan Ubangiji. Firistoci suna makoki, su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.
10 The field is devastated, the ground mourns; for the grain is destroyed, the new wine dries up, the oil fails. Filaye sun zama marasa amfani, ƙasa ta bushe; an lalatar da hatsi, sabon ruwan inabin ya bushe, mai kuma ba amfani.
11 Be ashamed, you farmers; wail, you grape growers, over the wheat and the barley, for the harvest of the field has perished. Ku fid da zuciya, ku manoma, ku yi ihu, ku masu noma inabi; ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir, saboda an lalata girbin filaye.
12 The vine is dried up, and the fig tree withers; the pomegranate, the palm, and the apple—all the trees of the field are dried up. Surely joy has withered away from all people. Kuringar inabin ta bushe itacen ɓaure kuma ya yi yaushi, ’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa, dukan itatuwan filaye, sun bushe. Tabbatacce farin cikin ’yan adam ya bushe.
13 Put on mourning clothes and lament, you priests; wail, you ministers of the altar. Come, spend the night in mourning clothes, you ministers of my Father; for the grain offering and the drink offering are withheld from the house of your Father. Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki; ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade. Zo, ku kwana saye da tsummoki, ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima, gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha daga gidan Allahnku.
14 Declare a fast; call a sacred assembly. Gather the elders and all who live in the land to the house of our Father, and cry out to our Father. Ku yi shelar azumi mai tsarki; ku kira tsarkakan taro. Ku kira dattawa da kuma dukan mazaunan ƙasar zuwa gidan Ubangiji Allahnku, ku kuma yi kuka ga Ubangiji.
15 Alas for the day! For the day of our Father is near, and it will come like destruction from the Almighty. Kaito saboda wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.
16 Is not the food cut off right before our eyes—joy and gladness gone from the house of our Father? Ba a yanke abinci a idanunmu, farin ciki da kuma murna daga gidan Allahnmu ba?
17 The seeds shrivel in the parched ground; the storehouses are desolate, the granaries are torn down, for the grain has dried up. Iri suna ta yanƙwanewa a busasshiyar ƙasa Ɗakunan ajiya sun lalace, an rurrushe rumbunan hatsin, gama hatsi ya ƙare.
18 How the animals groan! The herds of cattle wander in confusion because they have no pasture; even the flocks of sheep suffer. Ji yadda dabbobi suke nishi! Garkunan shanu sun ruɗe saboda ba su da ciyawa, har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
19 To you, our Father, I call, for fire has devoured the pastures of the wilderness, and flame has burned all the trees of the field. A gare ka, ya Ubangiji, nake kira, gama wuta ta cinye wurin kiwo harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.
20 Even the wild animals cry out to you, for the streams have dried up, and fire has devoured the pastures of the wilderness. Har ma namun jeji suna haki gare ka; rafuffuka sun bushe wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]