Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Isaiah 27 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Ceton Isra’ila

1A wannan rana,Ubangiji zai yi hukunci da takobi,takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna,zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe,dodon ruwa macijin nan mai murɗewa;zai kashe dodon nan na teku.

2A wannan rana,“Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce

3Ni, Ubangiji na lura da ita;na yi ta yin mata banruwa.Na yi tsaronta dare da ranadon kada wani yă yi mata ɓarna.

4Ban yi fushi ba.Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana!Zan fita in yi yaƙi da su;da na sa musu wuta duka.

5Ko kuma bari su zo wurina don mafaka;bari su yi sulhu da ni,I, bari su yi sulhu da ni.”

6A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa,Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fureya cika dukan duniya da ’ya’ya.

7Ubangiji ya buge shikamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi?An kashe shikamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?

8Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi,da tsananin tsawa kuma ka kore shi,kamar a ranar da iskar gabas ta hura.

9A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub,wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa.Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagadesuka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu,har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turareda za a bari a tsaye.

10Birni mai katanga ya zama kufai,yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada;a can ’yan maruƙa suke kiwo,a can suke kwance;sun kakkaɓe rassanta ƙaf.

11Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye sumata kuma su zo su yi itacen wuta da su.Gama mutane ne marar azanci;saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba,Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.

12A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya. 13Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]