Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Hebrews 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 So, holy brothers sharing a heavenly call, consider Jesus, the apostle and high priest we confess. Saboda haka, ’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa.
2 He was faithful to the one who appointed him, as Moses also was in all our Father's house. Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah.
3 Jesus deserves far more glory than Moses, as a house's builder deserves more honor than the house itself. An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.
4 For every house is built by someone, but the builder of all things is our Father. Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.
5 Moses was faithful in all our Father's house, a servant testifying to what would be spoken later. Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.
6 But Christ, as son, is faithful over his house. And we are his house—if we hold firm the confidence and hope we boast in. Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.
7 So, as the Holy Spirit says: "Today, if you hear his voice, Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,
8 do not harden your hearts as you did in the rebellion, on the day of testing in the wilderness, kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada,
9 where your ancestors put me to the test and saw my works for forty years. inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.
10 That is why I was angry with that generation, and I said, 'Their hearts are always going astray, and they have not known my ways.' Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’
11 So I swore in my anger, 'They will never enter my rest.'" Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”
12 Brothers, watch that none of you has an evil, unbelieving heart that deserts the living Father. Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.
13 But encourage each other daily, while it is called "today," so none of you becomes hardened by sin's deceit. Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.
14 For we have become sharers in Christ, if we truly keep our first confidence firm to the end. Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe.
15 As it is said: "Today, if you hear his voice, do not harden your hearts as when you rebelled." Kamar yadda aka faɗa cewa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a tawayen nan.”
16 Who heard and rebelled? Wasn't it all who left Egypt through Moses? Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba?
17 With whom was he angry forty years? Was it not with those who sinned, whose bodies fell in the wilderness? Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arba’in? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba?
18 Who did he swear would never enter his rest, except those who disobeyed? Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba?
19 So we see they couldn't enter because of lack of faith. Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]