Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Philemon 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Paul, a prisoner of Christ Jesus, and Timothy our brother, to Philemon, our dear friend and co-worker, Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,
2 and to our sister Apphia, our fellow soldier Archippus, and the church that meets in your house: zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.
3 Grace and peace to you from our Father and the Lord Jesus Christ. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
4 I always thank my Father as I remember you in my prayers, Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina,
5 because I hear of your love and faith in the Lord Jesus and for all his holy people. domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.
6 I pray your shared faith becomes effective as you come to understand every good thing we have in Christ. Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.
7 Your love has brought me great joy and comfort, brother, since you've refreshed the hearts of his holy people. Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.
8 Therefore, although in Christ I am bold enough to command you to do what is right, Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata,
9 instead, for love's sake I appeal—I, Paul, an old man, now also a prisoner of Christ Jesus. duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.
10 I appeal to you for my child Onesimus, whose father I became while I was in chains. Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi.
11 He was once useless to you, but now is useful to you and me. Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.
12 I am sending him back to you—and in doing so I am sending my very heart. Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata.
13 I wanted to keep him with me, to serve me on your behalf while I'm in chains for the gospel. Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara.
14 But I wanted to do nothing without your consent, so your good deed would not be forced, but voluntary. Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba.
15 Perhaps this is why he was separated from you briefly, so you'd have him back forever. Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani
16 No longer as a slave, but more than a slave—a beloved brother, especially to me, but even more to you, both in the flesh and in the Lord. ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.
17 So if you consider me a partner, welcome him as you would welcome me. Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni.
18 If he wronged you at all, or owes anything, put it on my account. In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina.
19 I, Paul, write this with my own hand: I'll repay it—not to mention you owe me yourself as well. Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi.
20 Yes, brother, do me this favor in the Lord—refresh my heart in Christ. Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi.
21 Trusting you'll obey, I write to you, knowing you'll do even more than I ask. Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.
22 Also prepare a guest room for me—I hope through your prayers to be graciously given back to you. Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.
23 Epaphras, my fellow prisoner in Christ Jesus, sends you greetings, Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.
24 and so do Mark, Aristarchus, Demas, and Luke, my fellow workers. Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.
25 The grace of the Lord Jesus Christ be with your spirit. Amen. Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]