Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Hebrews 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Long ago, in many times and many ways, our Heavenly Father spoke to our ancestors through the prophets. A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,
2 But in these final days he spoke to us by his Son, whom he appointed heir of all things and through whom he made the universe. amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya.
3 The Son is the brightness of our Father's glory, the exact image of his being, sustaining all things by his powerful word. After purifying sins, he sat down at the right hand of the Majesty on high. Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.
4 He became as much greater than angels as his inherited name is greater than theirs. Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.
5 For to which of the angels did our Father ever say, "You are my Son; today I have become your Father"? Or again, "I will be his Father, and he will be my Son"? Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”?
6 And again, when he brings the firstborn into the world, he says, "Let all my angels worship him. Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce, “Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”
7 Of the angels he says, "He makes his angels winds, and his servants flames of fire." Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce, “Ya mai da mala’ikunsa iska, bayinsa kuma harsunan wuta.”
8 But about the Son he says, "Your throne, O God, is forever and ever, and the scepter of righteousness is the scepter of your kingdom. Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka.
9 You have loved righteousness and hated wickedness; therefore our Father, your Father, has anointed you with the oil of gladness above your companions." Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka, ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”
10 And, "In the beginning, Lord, you laid the foundations of the earth, and the heavens are the work of your hands. Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.
11 They will perish, but you remain; they will all wear out like a garment. Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga.
12 You will roll them up like a robe; like a garment they will be changed. But you are the same, and your years will never end." Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”
13 But to which of the angels did our Father ever say, "Sit at my right hand until I make your enemies a footstool for your feet"?" Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka”?
14 Aren't all angels ministering spirits, sent to serve those about to inherit salvation? Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]