Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 When Moses finished setting up the tabernacle, he anointed and dedicated it and all its furnishings, the altar and all its utensils, anointing and dedicating them. Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.
2 Then Israel's leaders—heads of their fathers' houses, the tribal leaders in charge of the census—brought an offering. Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.
3 They brought their offering before our Father: six covered wagons, twelve oxen—a wagon per two leaders, an ox for each—then presented them before the tabernacle. Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.
4 And our Father said to Moses, Ubangiji ya ce wa Musa,
5 "Take these from them for the tent of meeting's service; give them to the Levites, each according to his service." “Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”
6 So Moses took the wagons and the oxen and gave them to the Levites. Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa.
7 Two wagons and four oxen he gave to the sons of Gershon, according to their service. Ya ba wa Gershonawa, kekunan yaƙi biyu da shanu huɗu bisa ga aikinsu,
8 He gave four wagons and eight oxen to Merari's sons, for their service, under Ithamar son of Aaron the priest. ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist.
9 To the sons of Kohath he gave none, since the holy things' service was theirs—carried on the shoulder. Amma Musa bai ba wa Kohatawa kome ba, gama aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.
10 On the day the altar was anointed, the leaders brought its dedication offering; the leaders brought their offering before the altar. Sa’ad da aka shafe bagaden da mai, sai shugabannin suka kawo hadayunsu saboda keɓewarsa, suka miƙa su a bagaden.
11 And our Father said to Moses, "Each day one leader is to bring his offering for the altar's dedication." Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Kowace rana, shugaba guda zai kawo hadayarsa saboda keɓewar bagade.”
12 Nahshon son of Amminadab, of Judah's tribe, presented his offering on the first day. Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda.
13 His offering: one silver plate, about three and a quarter pounds, and one silver basin, about one and three-quarter pounds, both filled with fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri ne, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
14 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; ya kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
15 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
16 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
17 for the peace offering: two oxen, five rams, five male goats, five year-old male lambs. This was Nahshon son of Amminadab's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.
18 On the second day Nethanel son of Zuar, the leader of Issachar, presented an offering. A rana ta biyu, Netanel ɗan Zuwar, shugaban mutanen Issakar, ya kawo hadayarsa.
19 His offering: one silver plate weighing about three and a quarter pounds, one silver bowl weighing about one and three-quarter pounds, both filled with fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
20 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel, goma cike da turaren hayaƙi;
21 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
22 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
23 for the peace offering: two oxen, five rams, five male goats, five year-old male lambs. This was Nethanel son of Zuar's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuwar.
24 On the third day it was Eliab son of Helon, the leader of the sons of Zebulun. A rana ta uku, Eliyab ɗan Helon, shugaban mutanen Zebulun, ya kawo hadayarsa.
25 His offering: one silver plate weighing about three and a quarter pounds, one silver basin weighing about one and three-quarter pounds, both full of fine flour mixed with oil for a grain offering; Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
26 one gold dish weighing about four ounces, full of incense; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
27 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
28 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
29 for the peace offering sacrifice: two oxen, five rams, five male goats, five male lambs a year old. This was Eliab son of Helon's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon.
30 On the fourth day it was Elizur son of Shedeur, the leader of the sons of Reuben. A ranan ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban mutanen Ruben, ya kawo hadayarsa.
31 His offering: one silver plate, about three and a quarter pounds, and one silver basin, about one and three-quarter pounds—both full of fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
32 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
33 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
34 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
35 and for the peace offering sacrifice: two oxen, five rams, five male goats, five male lambs a year old. This was Elizur son of Shedeur's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur.
36 On the fifth day it was Shelumiel son of Zurishaddai, the leader of the sons of Simeon. A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban mutanen Simeyon, ya kawo hadayarsa.
37 His offering: one silver plate, about three and a quarter pounds, one silver basin, about one and three-quarter pounds, both full of fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
38 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
39 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
40 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
41 for the sacrifice of peace offerings: two oxen, five rams, five male goats, five year-old male lambs. This was Shelumiel son of Zurishaddai's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai.
42 On the sixth day it was Eliasaph son of Deuel, the leader of the sons of Gad. A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deyuwel, shugaban mutanen Gad, ya kawo hadayarsa.
43 His offering was one silver plate, about three and a quarter pounds, and one silver basin, about one and three-quarter pounds, both filled with fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
44 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
45 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
46 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
47 for the peace offering: two oxen, five rams, five male goats, five male yearling lambs. This was Eliasaph son of Deuel's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deyuwel.
48 On the seventh day it was Elishama son of Ammihud, the leader of the sons of Ephraim. A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban mutanen Efraim, ya kawo hadayarsa.
49 His offering: one silver plate, about three and a quarter pounds, and one silver basin, about one and three-quarter pounds, both filled with fine flour mixed with oil for a grain offering; Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
50 one gold dish weighing about four ounces, full of incense; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
51 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
52 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
53 for the sacrifice of peace offerings: two oxen, five rams, five male goats, five male lambs a year old. This was Elishama son of Ammihud's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud.
54 On the eighth day it was Gamaliel son of Pedahzur, the leader of the sons of Manasseh. A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban mutanen Manasse, ya kawo hadayarsa.
55 His offering: one silver plate, about three and a quarter pounds, and one silver basin, about one and three-quarter pounds, both full of fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
56 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
57 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
58 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
59 for the peace offering: two oxen, five rams, five male goats, five year-old male lambs. Offering of Gamaliel son of Pedahzur. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur.
60 On the ninth day it was Abidan son of Gideoni, the leader of the sons of Benjamin. A rana ta tara, Abidan ɗan Gideyoni, shugaban mutanen Benyamin, ya kawo hadayarsa.
61 His offering: one silver plate, about three and a quarter pounds, one silver basin, about one and three-quarter pounds, both full of fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
62 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
63 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
64 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
65 for the peace-offering sacrifice: two oxen, five rams, five male goats, five yearling male lambs. This was Abidan son of Gideoni's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gideyoni.
66 On the tenth day it was Ahiezer son of Ammishaddai, the leader of the sons of Dan. A rana ta goma, Ahiyezer ɗan Ammishaddai, shugaban mutanen Dan, ya kawo hadayarsa.
67 His offering: one silver plate weighing about three and a quarter pounds, one silver basin weighing about one and three-quarter pounds, both full of fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
68 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
69 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
70 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
71 for the peace-offering sacrifice: two oxen, five rams, five male goats, five male year-old lambs. This was Ahiezer son of Ammishaddai's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahiyezer ɗan Ammishaddai.
72 On the eleventh day it was Pagiel son of Ochran, the leader of the sons of Asher. A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa.
73 He offered a silver plate, about three and a quarter pounds, and a silver basin, about one and three-quarter pounds, both filled with fine flour mixed with oil for a grain offering; Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
74 one gold dish weighing about four ounces, full of incense; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
75 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
76 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
77 and for the sacrifice of peace offerings: two oxen, five rams, five male goats, five male lambs a year old. The offering of Pagiel son of Ochran. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.
78 On the twelfth day it was Ahira son of Enan, the leader of the sons of Naphtali. A rana ta goma sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban mutanen Naftali, ya kawo hadayarsa.
79 His offering: one silver plate, about three and a quarter pounds, and one silver basin, about one and three-quarter pounds, both filled with fine flour mixed with oil for a grain offering. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
80 One gold dish weighing about four ounces, full of incense; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
81 one young bull, one ram, and one male lamb a year old, for a burnt offering; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
82 one male goat for a sin offering; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
83 and for the peace-offering sacrifice: two oxen, five rams, five male goats, five male lambs a year old. Ahira son of Enan's offering. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.
84 This was the altar's dedication offering when it was anointed, from Israel's leaders: twelve silver plates, twelve silver basins, twelve gold dishes. Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu.
85 Each silver plate weighed about three and a quarter pounds, each basin about one and three-quarter pounds; all the silver of the vessels totaled about sixty pounds. Kowane faranti na azurfa yana da nauyin shekel ɗari da talatin, kuma kowane daro na azurfa don yayyafawa yana da nauyin shekel saba’in. Duka-duka dai, nauyin kwanonin azurfa, shekel dubu biyu ne da ɗari huɗu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
86 The twelve gold dishes full of incense weighed about four ounces each; all the gold totaled about three pounds. Kwanonin zinariya goma sha biyu da aka cika da turaren hayaƙi kuwa, nauyinsu shekel goma ne kowanne, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duka-duka dai, nauyin kwanonin zinariya, shekel ɗari ɗaya ne da ashirin.
87 All the cattle for the burnt offering: twelve bulls, twelve rams, twelve year-old male lambs, with their grain offering; and twelve male goats for the sin offering. Jimillar dabbobi don hadaya ta ƙonawa, ta kai ƙanana bijimai goma sha biyu, raguna goma sha biyu da ’yan raguna goma sha biyu, dukansu bana ɗaya-ɗaya, tare da hadayarsu ta hatsi. Aka yi amfani da bunsurai goma sha biyu domin hadaya don zunubi.
88 All the cattle for the peace offering sacrifices: twenty-four bulls, sixty rams, sixty male goats, sixty male year-old lambs. This was the altar's dedication offering, after it was anointed. Jimillar dabbobi don hadaya ta salama, ta kai shanu ashirin huɗu, raguna sittin, bunsurai sittin da kuma ’yan raguna sittin, dukansu bana ɗaya-ɗaya. Waɗannan su ne hadayu saboda keɓewar bagade, bayan an shafe shi.
89 When Moses entered the tent of meeting to speak with our Father, he heard the voice speaking to him from above the mercy seat on the ark of the testimony, between the two cherubim—so our Father spoke with him. Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]