Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 6 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Then our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
2 "Speak to the Israelites and say to them: When a man or woman makes a special vow, a Nazirite vow, to set themselves apart to the Father. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,
3 They must not drink wine or strong drink, nor vinegar from either, nor any grape juice, nor eat grapes fresh or dried. dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.
4 During their separation they must eat nothing from the grapevine, from seeds to skin. Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.
5 "During their vow of separation, no razor touches their head. Until it's complete, they stay holy to the Father; they must let their hair grow. “ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.
6 "Throughout their time of separation to the Father they must not go near a dead body. A dukan kwanakin keɓewarsa ga Ubangiji, Banazarin ba zai yi kusa da gawa ba.
7 They must not make themselves unclean even for father, mother, brother, or sister when they die, since their dedication crown to our Father is on their head. Ko da ma gawar ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan mahaifiyarsa, ko kuma ta ’yar’uwarsa ce, ba zai ƙazantar da kansa saboda su ba, domin alamar keɓewarsa ga Allah tana kansa.
8 Throughout their time of separation they are holy to the Father. A dukan kwanakin keɓewarsa, an tsarkake shi ga Ubangiji.
9 "If someone dies very suddenly beside them, making their dedicated head unclean, they must shave their head on the day of their cleansing—shave it on the seventh day. “ ‘In farat ɗaya wani ya mutu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, dole yă aske kansa a ranar tsarkakewarsa, a rana ta bakwai.
10 On the eighth day they must bring two turtledoves or two young pigeons to the priest at the meeting tent's entrance. Sa’an nan a rana ta takwas, tilas yă kawo wa firist ’yan kurciyoyi biyu, ko kuma ’yan tattabarai biyu a bakin ƙofar Tentin Sujada.
11 The priest must offer one as a sin offering, the other as a burnt offering, and make atonement for them, because they sinned by being near the dead body. That same day they must rededicate their head. Firist kuwa zai miƙa ɗaya don hadaya ta zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa, yă yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi ta dalilin gawar. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.
12 They must rededicate to the Father their days of separation and bring a year-old male lamb as a guilt offering; the earlier days don't count—their separation was made unclean. Dole yă keɓe kansa ga Ubangiji, har kwanakin keɓewarsa, kuma dole yă kawo ɗan rago bana ɗaya a matsayin hadayar laifi. Kwanakin baya ba sa cikin lissafi, domin ya ƙazantu a lokacin keɓewarsa.
13 "This is the law of the Nazirite: when their days of separation end, they must come to the tent of meeting's entrance. “ ‘To, ga doka saboda Banazare sa’ad da kwanakin keɓewarsa suka gama. Za a kawo shi a bakin ƙofar Tentin Sujada.
14 They must bring the Father their offering: one flawless year-old male lamb as a burnt offering, one flawless year-old ewe lamb as a sin offering, and one flawless ram as a peace offering, A can zai miƙa hadayunsa ga Ubangiji. Hadayun kuwa su ne, ɗan rago, bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ’yar tunkiya, bana ɗaya marar lahani na hadaya don zunubi, rago marar lahani don hadaya ta salama,
15 with a basket of unleavened bread—loaves of fine flour mixed with oil, unleavened wafers coated with oil—plus their grain offering and drink offerings. tare da hadayu na hatsi da hadayu na sha, da kuma kwando burodi marar yisti, ƙosai da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da kuma wainan da aka barbaɗa da mai.
16 The priest must present them before the Father and offer the sin offering and the burnt offering. “ ‘Firist zai kawo su a gaban Ubangiji, yă miƙa hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa.
17 He must offer the ram as a peace offering to the Father with the basket of bread without yeast, and offer its grain and drink offerings. Zai miƙa kwandon burodi marar yisti, yă kuma miƙa ɗan ragon hadaya ta salama tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha ga Ubangiji.
18 At the tent of meeting's entrance, the Nazirite must shave their dedicated head, take the hair of dedication, and put it on the fire under the peace offering. “ ‘Sa’an nan a ƙofar Tentin Sujada, dole Banazaren yă aske gashin da ya alamta keɓewarsa, yă kwashe gashin, yă zuba a cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.
19 The priest takes the boiled ram's shoulder, one unleavened loaf and wafer from the basket, and puts them in the Nazirite's hands after the hair of dedication is shaved off. “ ‘Bayan Banazaren ya aske gashinsa da ya alamta keɓewa, firist zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar rago, da ƙosai da kuma waina daga cikin kwando waɗanda duka biyu marar yisti ne, yă sa su a tafin hannun keɓaɓɓen.
20 The priest waves them as a wave offering before our Father—a holy portion for the priest, with the breast that is waved and the thigh that is contributed. Then the Nazirite may drink wine. Firist zai kaɗa su a gaban Ubangiji, hadaya ce ta kaɗawa; mai tsarki ne kuma, zai zama na firist, tare da ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka kawo. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi.
21 "This is the law of the Nazirite who vows an offering to our Father for their separation, besides whatever else they can afford. They must do according to their vow, per the law of their separation." “ ‘Wannan ita ce dokar Banazare wanda ya yi alkawari ga Ubangiji bisa ga keɓewarsa, tare da duk abin da zai iya bayarwa. Tilas yă cika alkawarin da ya yi bisa ga dokar zaman Banazare.’ ”
22 Then our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
23 "Tell Aaron and his sons: This is how you are to bless the Israelites. Say to them: “Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu,
24 'May your Father bless you and keep you; “ ‘ “Ubangiji yă albarkace ku, yă kuma kiyaye ku;
25 may your Father make his face shine upon you and be gracious to you; Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku, yă kuma yi muku alheri;
26 may your Father look on you with favor and give you peace.' Ubangiji yă dube ku da idon rahama, yă kuma ba ku salama.” ’
27 "So they will put my name on the Israelites, and I will bless them." “Da haka za su sa sunana a kan Isra’ilawa, ni kuma zan albarkace su.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]