Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
2 "Command the Israelites to send from the camp everyone with a skin disease, everyone with a discharge, and everyone unclean from a corpse. “Ka umarci Isra’ilawa su kori duk wanda yake da ciwon fatan jiki, ko mai ɗiga na kowane iri, ko wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin sansani.
3 Send away both male and female; send them outside the camp, so they don't make their camp unclean, where I live among them." Ka kori maza da mata ma; ka kai su bayan sansani domin kada su ƙazantar da sansani inda nake zama a cikinsu.”
4 The Israelites did this, sending them outside the camp; as our Father told Moses, the Israelites did. Isra’ilawa suka yi haka; suka kore su daga sansanin. Suka aikata yadda dai Ubangiji ya umarci Musa.
5 Then our Father spoke to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
6 "Tell Israel's people: When a man or woman commits any human sin, betraying me, that person is guilty. “Gaya wa Isra’ilawa, ‘Sa’ad da namiji ko mace ya yi wa ɗan’uwansa laifi ta kowace hanya, ta yin haka, ya yi rashin aminci ga Ubangiji, mutumin kuwa ya yi laifi ke nan
7 They must confess the sin they committed, repay in full for the wrong, add a fifth, and give it to the one they wronged. kuma dole yă furta zunubin da ya yi. Dole yă yi biya cikakkiyar diyya saboda laifinsa, yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar a kai, yă kuma bayar da shi duka ga wanda ya yi wa laifin.
8 But if that person has no relative to receive restitution, it belongs to me and goes to the priest, plus the ram of atonement made for the guilty one. Amma in mutumin da aka yi wa laifin ba shi da ɗan’uwa na kusa da za a biya diyya saboda laifin, sai diyyar tă zama ta Ubangiji, dole kuma a ba wa firist, haɗe da ragon da za a yi kafara da shi.
9 Every contribution among all Israel's holy gifts brought to the priest belongs to him. Dukan tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka kawo wa firist za su zama nasa.
10 Everyone's holy gifts remain their own; what one gives the priest belongs to the priest." Kowace tsarkakakkiyar kyauta da mutum ya kawo nasa ne, sai dai abin da ya ba wa firist, zai zama na firist.’ ”
11 Then our Father spoke to Moses: Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
12 "Speak to the Israelites and tell them: If any man's wife goes astray and is unfaithful to him, “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In matar wani ta kauce, ta kuma yi rashin aminci gare shi
13 if another man sleeps with her, hidden from her husband, and she goes undetected though unclean—no witness against her, not caught in the act, ta wurin kwana da wani dabam, wannan kuwa ya kasance a ɓoye ga mijinta, rashin tsarkinta kuwa bai tonu ba (da yake babu shaida, ba a kuma kama ta tana yi ba),
14 a spirit of jealousy comes over the husband, and he is jealous of his wife, who is unclean; or a spirit of jealousy comes over him, and he is jealous though she is not unclean. in kuma kishi ya sha kan mijinta kuma tana da ƙazanta, ko kuwa idan yana kishi yana kuma zatonta ko ma ba ta da ƙazanta
15 The man must bring his wife to the priest, along with her offering: about two quarts of barley flour. He must pour no oil on it and put no frankincense on it, because it is a grain offering of jealousy, a grain offering of remembrance, recalling guilt. mijin zai kai matansa a gaban firist, yă kuma kawo hadayar abubuwan da ake bukata; abubuwa kamar, garin sha’ir garwa ɗaya, amma kada yă zuba mai a kan garin sha’ir, kada kuma yă sa turaren wuta a kansa, domin hadaya ce ta miji mai tuhumar matarsa da aka kawo domin gaskiya tă fito fili.
16 The priest is to bring her near and set her before our Father. “ ‘Firist zai kawo ta, yă sa tă tsaya a gaban Ubangiji.
17 The priest is to take holy water in a clay jar, take dust from the tabernacle floor, and put it into the water. Sa’an nan zai ɗebi ruwa mai tsarki a tulun laka, yă zuba ƙurar da ya ɗebo daga daɓen tabanakul a cikin ruwan.
18 The priest is to stand the woman before our Father, unbind her hair, and put in her hands the grain offering of remembrance—the jealousy offering—while he holds the bitter, curse-bringing water. Bayan da firist ya sa matan ta tsaya a gaban Ubangiji, sai yă kunce gashin kanta, yă kuma sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi, yayinda shi kansa zai riƙe ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana.
19 The priest is to put her under oath and say to her: 'If no man has slept with you, and you have not gone astray and made yourself unclean under your husband's authority, be free from this bitter water that brings the curse. Sa’an nan firist zai sa tă yi rantsuwa, yă kuma ce mata, “In ba wani mutumin da ya kwana da ke kuma ba ki kauce kin ƙazantar da kanki yayinda kike auren mijinki ba, kada wannan ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, yă cuce ki.
20 But if you strayed under your husband, made yourself unclean, and a man besides your husband slept with you.' Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,”
21 Then the priest is to bind the woman by this curse-oath, saying: May the Father turn you into a curse and a disgrace among your people, as he makes your thigh shrivel and your belly swell. (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura.
22 May this curse-bringing water enter your body, swelling your belly and wasting your thigh. Then the woman must say, 'Amen, amen.' Bari wannan ruwa mai jawo la’ana, yă shiga jikinki saboda cikinki yă kumbura, cinyarki kuma yă shanye.” “ ‘Sai macen tă ce, “Amin. Bari yă zama haka.”
23 "Then the priest writes these curses on a scroll and washes them off into the bitter water. “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci.
24 He is to make the woman drink the bitter, cursing water; the cursing water will enter her, causing bitter suffering. Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi.
25 The priest takes the jealousy grain offering from her hand, waves it before our Father, and brings it to the altar. Firist zai karɓi hadaya ta gari don kishi daga hannuwanta, yă kaɗa shi a gaban Ubangiji sa’an nan yă kawo a bagade.
26 The priest takes a handful of the grain offering, its memorial portion, burns it on the altar, then makes the woman drink the water. Sa’an nan firist zai ɗiba hatsi na hadaya cike da hannunsa don hadayar tunawa, yă kuma ƙone a bagade; bayan haka sai yă sa macen tă sha ruwan.
27 After he makes her drink the water, if she has made herself unclean and betrayed her husband, the curse-bringing water will enter her, causing bitter suffering: her belly will swell, her thigh wither, and she will become a curse among her people. In ta ƙazantar da kanta ta kuma ci amanar mijinta, to, yayinda aka sa tă sha ruwa mai jawo la’ana, ruwan zai shiga cikinta, yă jawo mata wahala mai zafi; cikinta zai kumbura, cinyarta kuma yă shanye, tă kuwa zama la’ananniya a cikin mutanenta.
28 But if the woman has not made herself unclean and is clean, she is cleared and will conceive children. Amma fa, in macen ba tă ƙazantar da kanta ba, ba tă kuma da ƙazanta, za a kuɓutar da ita daga laifin, za tă kuma iya haihuwa.
29 "This is the law of jealousy: when a wife under her husband strays and makes herself unclean, “ ‘Wannan dai, ita ce dokar kishi sa’ad da mace ta kauce, ta kuma ƙazantar da kanta yayinda take aure da mijinta,
30 or when a spirit of jealousy seizes a man and he is jealous of his wife: he is to stand her before our Father, and the priest is to apply this whole law to her. ko kuma sa’ad da mijin yana kishi domin yana shakkar matarsa. Firist zai sa tă tsaya a gaban Ubangiji, yă kuma yi amfani da wannan doka gaba ɗaya a kanta.
31 The husband will be free from guilt, but the woman will answer for her own sin." Mijin zai zama marar laifi daga kowane laifi, amma matar za tă ɗauki muguntarta, idan ta yi laifin.’ ”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]