Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father spoke to Moses and Aaron, saying: Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
2 "Count the Kohathites among the Levites, by clan and ancestral house. “Ku yi ƙidaya Kohatawa daga Lawiyawa, bisa ga kabilarsu da iyalansu.
3 From thirty to fifty years old, all who enter the service to work in the tent of meeting. Ku ƙidaya dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin da suka zo domin aiki a Tentin Sujada.
4 "This is the service of Kohath's sons in the tent of meeting: the most holy things. “Ga aikin Kohatawa a Tentin Sujada, kulawa da kayayyaki mafi tsarki.
5 When the camp moves, Aaron and his sons take down the screening curtain and cover the ark of the testimony with it. Lokacin da za a tashi daga sansani, Haruna da ’ya’yansa za su shiga ciki su kunce labulen kāriya, su rufe Akwatin Alkawari da shi.
6 They are to cover it with fine leather, spread an all-blue cloth over that, and set its poles. Sa’an nan su rufe shi da fatun shanun teku, su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi a bisansa, su sa masa sandunansa.
7 "On the table of the Presence they'll spread a blue cloth, put the plates, dishes, bowls, and pouring jars on it; the regular bread stays on it. “A bisa teburin Burodin Ajiyewa, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, a kansa kuma su sa farantai, kwanoni da manyan kwanoni, da tuluna don hadayun sha; da burodin da zai ci gaba da kasancewa a kansa.
8 They are to spread a scarlet cloth over them, cover it with fine leather, and fit its poles. A bisa waɗannan za su shimfiɗa jan zane, su rufe su da fatun shanun teku, su kuma zura masa sandunansa.
9 "They will take a blue cloth, cover the lampstand of light, its lamps, tongs, trays, and all its oil vessels used to service it. “Za su ɗauki zane mai ruwan shuɗi su rufe wurin ajiye fitilan da yake don fitilu, tare da fitilunsa, lagwaninsa da farantansa, da dukan tulunansa don man amfaninsu.
10 They are to wrap it and all its vessels in fine leather and set it on the carrying frame. Sa’an nan su naɗe shi da kuma dukan kayayyakinsa a cikin fatar shanun teku, su sa shi a kan sandan ɗaukarsa.
11 "Over the golden altar they are to spread blue cloth, cover it with fine leather, and insert its poles. “A kan bagaden zinariya, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, su kuma rufe shi da fatar shanun teku, sai a zura masa sandunansa.
12 They must take all the service utensils used in the sanctuary, put them in blue cloth, cover with fine leather, and place them on the pole. “Za su ɗauki dukan kayayyakin da ake amfani da su a wuri mai tsarki, su nannaɗe su da zane mai ruwan shuɗi, su rufe shi da fatar shanun teku, sa’an nan a sa su a kan sandan ɗaukarsa.
13 "They are to remove the ashes from the altar and spread a purple cloth over it. “Za su kwashe tokar da take a bagaden tagulla, su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi a bisansa.
14 On it they are to put all its serving vessels—firepans, forks, shovels, basins, all the altar's vessels—then spread over it a fine leather covering and insert its poles. Sa’an nan su sa a kansa dukan kayayyakin da aka yi amfani da su a bagaden, haɗe da farantai don wuta, cokula masu yatsu don nama, manyan cokula, da darunan yayyafawa. A kansa za su shimfiɗa murfi na fatun shanun teku, su zura sandunan ɗaukarsa.
15 "When Aaron and his sons finish covering the holy things and all vessels of the holy place, and the camp sets out, Kohath's sons come to carry them, but they must not touch the holy things or die. These are Kohath's sons' burdens in the tent of meeting. “Bayan Haruna da ’ya’yansa suka gama rufe kayayyaki masu tsarki da dukan abubuwa masu tsarki, sa’ad da kuma aka shirya tashi daga sansani, sai Kohatawa su zo gaba, su ɗauka. Amma kada su taɓa abubuwa masu tsarki, don kada su mutu. Kohatawa za su ɗauki abubuwan da suke cikin Tentin Sujada.
16 "Eleazar son of Aaron the priest is responsible for the lamp oil, fragrant incense, daily grain offering, and anointing oil—responsible for the whole tabernacle, everything in it, the sanctuary and its furnishings." “Eleyazar ɗan Haruna firist zai lura da man fitila da turare da hadaya ta gari na kullum da kuma keɓaɓɓen mai. Shi ne zai lura da dukan tabanakul da duk abin da yake cikinsa da kuma kayayyaki da abubuwan masu tsarki.”
17 Our Father spoke to Moses and Aaron, saying: Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
18 "Do not let the tribe of the Kohathite clans be cut off from among the Levites. “Ku tabbata cewa ba a kawar da zuriyar Kohatawa daga Lawiyawa ba.
19 Do this for them so they live and not die when they approach the most holy things: Aaron and his sons must enter, assigning each his task and burden. Saboda su rayu, kada su mutu sa’ad da suka zo kusa da abubuwa mafi tsarki, a yi musu wannan, wato, Haruna da ’ya’yansa za su shiga wuri mai tsarki su ba wa kowane mutum aikinsa da kuma abin da zai ɗauka.
20 But they must not go in and look at the holy things, even for a moment, or they will die." Amma kada Kohatawa su shiga don su dubi abubuwa masu tsarki, ko na ɗan ƙanƙanin lokaci, in ba haka ba za su mutu.”
21 Our Father spoke to Moses, saying: Ubangiji ya ce wa Musa,
22 "Take a census of the sons of Gershon also, by their fathers' houses and their clans. “Ka ƙidaya mutanen Gershon bisa ga iyalansu da kabilarsu.
23 Count those thirty to fifty years old who serve, doing work at the tent of meeting. Ka ƙidaya maza masu shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada.
24 "This is the service of the clans of the Gershonites, in serving and in carrying: “Ga aikin kabilar Gershonawa yayinda suke aiki, suke kuma ɗaukar kaya.
25 They carry the tabernacle's curtains, the tent of meeting, its covering, the fine-leather covering over it, and the screen for the tent of meeting's entrance, Za su ɗauki labulen tabanakul, Tentin Sujada, kayan da za a rufe shi, da kuma kayan da za a rufe shi daga waje na fatun rufuwa na shanun teku, labulen ƙofar Tentin Sujada,
26 the courtyard curtains, the entrance screen for the courtyard gate, surrounding tabernacle and altar, their cords, and all their service equipment—they are to do whatever these need. labulen filin da yake kewaye da tabanakul da bagade, labulen ƙofa, igiyoyi da kuma dukan abubuwan da ake amfani da su wajen hidima. Geshonawa za su yi dukan abin da ya kamata a yi da waɗannan abubuwa.
27 Aaron and his sons direct all the Gershonites' service—their carrying and duties; assign them all they must carry. Dukan hidimominsu, ko na ɗauko, ko kuma na yin wani aiki, za a yi su ne bisa ga umarnin Haruna da ’ya’yansa. Za ka ba su dukan kayan da za su ɗauka a matsayin hakkinsu.
28 This is the service of the Gershonite clans at the tent of meeting, their duty under Ithamar son of Aaron the priest. Wannan shi ne hidimar da kabilar Gershonawa za su yi a Tentin Sujada. Ayyukansu za su kasance bisa ga umarnin Itamar ɗan Haruna firist.
29 "As for the sons of Merari, you are to count them by their clans and their fathers' houses. “Ka ƙidaya kabilar Merari bisa ga kabilarsu da iyalansu.
30 Count everyone thirty to fifty years old who enters the service to work at the tent of meeting. Ka ƙidaya maza daga masu shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada.
31 This is their task, their service at the meeting tent: the frames, bars, posts, and bases of the tabernacle. Ga aikinsu sa’ad da suke hidima a Tentin Sujada, za su ɗauki katakan tabanakul, sandunansa da dogayen sandunansa, da rammukansa,
32 The courtyard's pillars all around, with their bases, pegs, and cords, all their equipment and service—assign by name what each must carry. har ma da dogayen sandunan kewayen filin da rammukansu, turakun tenti, igiyoyi, da dukan kayayyaki, da kuma dukan abubuwan da suke dangane da amfaninsu. Ka ba wa kowane mutum ayyuka na musamman da zai yi.
33 This is the Merarite clans' service in the Tent of Meeting, under Ithamar son of Aaron the priest." Wannan ce hidimar da mutanen Merari za su yi a aikin Tentin Sujada, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist.”
34 So Moses, Aaron, and the leaders of the congregation counted the sons of the Kohathites by their clans and their families, Musa, Haruna da kuma shugabannin jama’a, suka ƙidaya Kohatawa ta kabilarsu da kuma iyalansu.
35 thirty to fifty years old, all who joined the service for work in the tent of meeting. Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada,
36 Those counted by their clans were 2,750. da aka ƙidaya, kabila-kabila, su 2,750 ne.
37 The count of Kohathite clans, all who served in the tent of meeting, whom Moses and Aaron counted at our Father's command through Moses. Jimillar dukan waɗanda suke na kabilan Kohatawa, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada ke nan. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji.
38 Those counted of the sons of Gershon, by their clans and their fathers' houses, Aka ƙidaya mazan Gershonawa ta kabilansu da kuma iyalansu.
39 from thirty to fifty years old, all who entered service work at the tent of meeting. Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada,
40 Those counted by their clans and their fathers' houses were 2,630. da aka ƙidaya kabila-kabila da kuma iyali-iyali, su 2,630 ne.
41 These were counted from the Gershonite clans, all who served in the tent of meeting, whom Moses and Aaron counted at our Father's command. Jimillar waɗanda suke na kabilar Gershonawa ke nan, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji.
42 Those counted of the clans of the sons of Merari, by their clans and their fathers' houses, Aka ƙidaya mazan Merari ta kabilarsu da kuma iyalansu.
43 from age thirty to fifty, all who entered service for work in the tent of meeting, Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada,
44 those counted by their clans were 3,200. da aka ƙidaya kabila-kabila, su 3,200 ne.
45 These were counted of the clans of Merari's sons, whom Moses and Aaron counted at our Father's command through Moses. Jimillar waɗanda suke na kabilar Merari ke nan. Musa da Haruna suka ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji.
46 All those whom Moses, Aaron, and Israel's leaders counted among the Levites, by clans and ancestral houses. Saboda haka, Musa, Haruna da shugabannin Isra’ila, suka ƙidaya dukan Lawiyawa kabila-kabila da kuma iyali-iyali.
47 From thirty to fifty years old, everyone who served and carried loads in the tent of meeting. Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki da kuma ɗaukar Tentin Sujada
48 Those counted were 8,580. jimillarsu ta kai 8,580.
49 By our Father's command, Moses appointed each to his service and burden, and counted them, as our Father commanded Moses. Bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa, aka ba kowa aikinsa, aka kuma faɗa musu abin da za su ɗauka. Ta haka aka ƙidaya su, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]