Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 This is the family line of Aaron and Moses, when our Father spoke with Moses on Mount Sinai. Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa a lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai.
2 These are the names of the sons of Aaron: Nadab the firstborn, then Abihu, Eleazar, and Ithamar. Sunayen ’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar.
3 These are the names of Aaron's sons, the anointed priests whom Moses ordained to serve as priests. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Haruna, shafaffun firistocin da aka naɗa domin su yi aiki firist.
4 Nadab and Abihu died before our Father in the wilderness of Sinai when they offered unauthorized fire before him; they had no children. So Eleazar and Ithamar served as priests before Aaron their father. Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.
5 Then our Father said to Moses: Ubangiji ya ce wa Musa,
6 "Bring the tribe of Levi near and set them before Aaron the priest, to serve him. “Ka kawo mutanen Lawi, ka kuma gabatar da su ga Haruna firist, don su taya shi aiki.
7 They are to keep his duties and those of the whole community before the tent of meeting, performing the tabernacle's service. Za su yi wa Haruna da dukan al’umma aikace-aikace a Tentin Sujada, ta wurin yin aikin tabanakul.
8 They are to guard all the tent of meeting's equipment and the Israelites' duty, doing the tabernacle's service. Za su lura da dukan kayayyakin Tentin Sujada, suna cika hakkin Isra’ilawa ta wurin yin aiki a tabanakul.
9 Give the Levites to Aaron and his sons; they are given entirely to him from among Israel's people. Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da ’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi.
10 Appoint Aaron and his sons to guard their priesthood; any outsider who comes near must die." Ka naɗa Haruna da ’ya’yansa su yi aiki firistoci; duk wanda ya yi shisshigi a wuri mai tsarki kuwa dole a kashe shi.”
11 Then our Father said to Moses: Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
12 "Look, I have taken the Levites from among the Israelites in place of every firstborn that opens the womb among the Israelites. The Levites are mine. “Ga shi na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon ɗan fari na kowace mace a Isra’ila. Lawiyawa nawa ne,
13 Every firstborn is mine. The day I struck down every firstborn in Egypt, I set apart for myself every firstborn in Israel—both man and animal. They will be mine. I am your Father." gama duk ’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk ’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”
14 Then our Father spoke to Moses in the wilderness of Sinai: Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai ya ce,
15 "Count Levi's sons by fathers' houses and clans; count every male a month old and up." “Ka ƙidaya Lawiyawa bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya kowane ɗan jinjiri mai wata ɗaya ko fiye.”
16 So Moses counted them at the word of our Father, just as he had been commanded. Saboda haka Musa ya ƙidaya su duka, kamar yadda maganar Ubangiji ta umarta.
17 These were the sons of Levi by their names: Gershon, Kohath, and Merari. Ga sunayen ’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.
18 These are the names of the sons of Gershon by their clans: Libni and Shimei. Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi
19 The sons of Kohath by their clans: Amram, Izhar, Hebron, and Uzziel. Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
20 Merari's sons by clan: Mahli and Mushi. These are the Levite clans by fathers' houses. Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu.
21 From Gershon: the Libnite clan and the Shimeite clan—these are the Gershonite clans. A wajen Gershonawa, kabilarsa su ne Libniyawa, da Shimeyiyawa; waɗannan su ne mutanen Gershom.
22 The number of males counted, a month old or older, was 7,500. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500.
23 The clans of the Gershonites camped behind the tabernacle on the west. Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul.
24 The leader of the fathers' house of the Gershonites was Eliasaph son of Lael. Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa.
25 Gershon's sons at the tent of meeting cared for the tabernacle, the tent, its covering, and the entrance screen of the tent of meeting. A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada,
26 The courtyard's curtains and its entrance screen, surrounding the tabernacle and altar, and its cords for all its service. da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu.
27 From Kohath came the Amramite clan, the Izharite clan, the Hebronite clan, and the Uzzielite clan; these are the clans of the Kohathites. Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa.
28 Males a month old and up numbered 8,600, in charge of the sanctuary. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki.
29 The clans of the sons of Kohath camped on the south side of the tabernacle. Kohatawa za su yi sansani a kudu da tabanakul.
30 The leader of the fathers' house of the Kohathite clans was Elizaphan son of Uzziel. Shugaban kabilar Kohatawa shi ne Elizafan ɗan Uzziyel.
31 They cared for the ark, the table, the lampstand, the altars, the sanctuary vessels used in service, the screen, and all its work. Su ne da hakkin kula da akwatin alkawari, tebur, wurin ajiye fitila, bagade, kayayyakin wuri mai tsarki da ake amfani da su a sujada, labule, da kuma kome da ya danganci aikinsu.
32 Eleazar son of Aaron the priest was chief leader of the Levites, in charge of those guarding the sanctuary. Babban shugaban Lawiyawa shi ne Eleyazar ɗan Haruna, firist. An naɗa shi a kan waɗanda suke kula da wuri mai tsarki.
33 From Merari: the Mahlite clan and the Mushite clan—these are Merari's clans. Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari.
34 The number of males counted, a month old or older, was 6,200. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne.
35 Leader of Merarite clans' ancestral house: Zuriel son of Abihail; they camped on the tabernacle's north side. Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul.
36 Merari's sons were charged with the tabernacle's frames, crossbars, posts, bases, all its equipment, and all its service, Kabilar Merari ne aka sa su lura da katakan tabanakul, sandunanta, dogayen sandunanta, tarukanta, dukan kayan aiki da kowane abin da ya danganci aikinsu,
37 as well as the posts of the surrounding courtyard with their bases, pegs, and cords. da ginshiƙai kewaye da filin tare da rammuka da turaku da igiyoyinsu.
38 Camped east of the tabernacle, in front of the tent of meeting toward sunrise, were Moses, Aaron, and his sons, who kept charge of the sanctuary for the Israelites; any outsider who approached was to be put to death. Musa da Haruna da ’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi.
39 All the Levites whom Moses and Aaron counted at our Father's command, by their clans, every male a month old and up: 22,000. Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne.
40 Then our Father said to Moses, "Count every firstborn male of Israel a month old or older, and record the number of their names. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ƙidaya dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa maza daga wata ɗaya da kuma fiye ka kuma rubuta sunayensu.
41 Take the Levites for me—I am your Father—in place of every firstborn among the people of Israel, and the Levites' livestock in place of every firstborn among Israel's livestock." Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon ’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”
42 So Moses counted every firstborn among the people of Israel, just as our Father had commanded him. Haka Musa ya ƙidaya ’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
43 All firstborn males, a month or older, listed by name: 22,273. Jimillar ’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne.
44 Then our Father spoke to Moses: Sai Ubangiji ya kuma yi magana da Musa ya ce,
45 "Take the Levites instead of every firstborn among Israel's people, and the Levites' livestock instead of theirs. The Levites will be mine. I am your Father. “Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.
46 To redeem the 273 firstborn Israelites exceeding the Levites' count. Don a fanshi ’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa,
47 Collect about 2 ounces per person, by sanctuary standard (each measure about half an ounce of silver). ka karɓi shekel biyar domin kowannensu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda yake da nauyin gera ashirin.
48 Give the money to Aaron and his sons as the redemption price for the extra firstborn sons." Ka ba wa Haruna da ’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na ’ya’yan farin Isra’ilawa.”
49 So Moses collected the redemption money from the firstborn sons who exceeded the number of the Levites; Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.
50 from Israel's firstborn sons he took 1,365—about 2 ounces, by the sanctuary standard. Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
51 Moses gave the redemption money to Aaron and his sons, by our Father's word, just as our Father commanded Moses. Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da ’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]